A yau Litinin, kasar Sin ta sanar da sabbin ka’idojin kyautata kare sirrikan jama’a yayin kare tsaron al’umma.
Firaministan kasar Sin Li Qiang ne ya rattaba hannu kan wata dokar majalisar gudanarwar kasar, domin fitar da ka’idojin, wadanda za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Afrilu.
Ka’idojin na da nufin tafiyar da harkokin da suka shafi kula da tsare-tsaren kyamarorin da aka kafa domin tsaron al’umma da kare sirrika da hakkoki da muradu da ma bayanan daidaikun mutane. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)