Kamfanin kula da sufurin layin dogo na kasar Sin, ya ce jarin manyan kadarori da kasar ta zuba a bangaren layin dogo ya kai yuan biliyan 43.9, kwatankwacin dala biliyan 6.12, a watan Janairun bana.
A cewar kamfanin, adadin ya karu da kaso 3.7 bisa dari idan aka kwatantan da makamancin lokacin a bara.
A wannan lokaci, an gudanar da manyan ayyuka, ciki har inganta layin dogo mai saurin tafiya tsakanin biranen Chengdu da Chongqing. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)