Kungiyar kula da harkokin jigilar kayayyaki da sayen kayayyaki ta kasar Sin ta samar da adadin sana’o’in adana kayayyaki na Sin a watan Janairun da ya gabata cewa, wanda ya nuna cewa, yawan bukatun ajiye kaya a Sin ya bunkasa cikin sauri duba da karuwar bukatun sayayya a lokacin bikin sabuwar shekara, kuma sana’o’in adana kayayyaki na ci gaba da samun bunkasuwa.
Adadin sana’o’in adana kayayyaki na Sin ya kai kashi 52.5%, a watan Janairun da ya wuce, wanda ya karu da kashi 1.9% bisa na watan Disamban da ya gabata, adadin da ya kai koli a cikin watanni 10 da suka gabata.
Sakamakon manufofin tabbatar da tattalin arziki da ingiza bunkasuwa, da ma yadda aka koma aiki bayan hutun bikin sabuwar shekara ta Sinawa, an yi kiyasin cewa, sana’o’in adana kayayyaki za su ci gaba da samun bunkasuwa ba tare da tangarda ba. (Amina Xu)