Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC ta rufe shaguna, da wuraren ajiya da ake zargin ana sayar da magunguna da sauran kayayyakin kiwon lafiya marasa inganci.
An kuma tafi da wasu magunguna da wasu kayayyakin kiwon lafiya da ake zargin marasa inganci ne domin tabbatarwa.
Shugaban hukumar ta NAFDAC tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun ziyarci kasuwar magunguna da ke idumota a jihar Legas a kokarin da suke na tsaftace kayayyakin kiwon lafiya na kasa.