Wani abu da ya ja hankalina kuma ya jefa ni cikin tunani a kan abubuwan da ke faruwa a kan batun kare-karen harajin kwastam da Amurka ke yi a kan kayayyakin da ake shigo da su kasarta shi ne, yadda shahararren kamfanin nan na kera motoci na Amurka Tesla ya fara aiki kwanan nan a katafariyar masana’antar da ya gina a birnin Shanghai, babbar cibiyar hada-hadar kasuwanci ta kasar Sin.
Wannan ya nuna yadda kamafanin yake kara fadada harkokinsa na kasuwanci a kasar Sin. Kuma saboda yadda kamfanin ya samu saukin gudanar da harkokinsa albarkacin manufar kasar Sin ta kara bude kofarka ga kasashen waje, domin su shigo a dama da su a kasuwarta ta amfani da kayayyaki mafi girma a duniya, cikin watanni takwas kacal da fara aikin gidana sabuwar masana’antar, tuni har an fara sarrafa kayayyakin kamfanin gadan-gadan.
- Kasar Sin Ta Yi Kiran Samar Da Ci Gaba Da Tsaro Bai-daya A Fannin Fasahar AI
- Babu Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Tsarinmu – Gwamnan Zamfara
Masana’antar za ta fi mayar da hankali ce ga samar da manyan baturan makamashi da aka fi sani da “megapacks” inda za ta rika kera rukunan batura a kalla 10,000 masu makamashin da ya kai karfin sa’o’in gigawatt 40, a duk shekara a farkon fara aiki.
Fadin kadadar filin kamfanin ya kai murabba’in mita 200,000, kana jarin da aka zuba a sabuwar masana’antar ya kai dala miliyan 202 wanda tabbas manuniya ce ga irin amincin da kamfanonin Amurka suka samu a kasar Sin na gudanar da harkokinsu ba tare da fargaba ba.
Kazalika, ba kamfanin Tesla ne kawai yake cin moriyar kasar Sin ba, akwai wasu kamfanonin Amurka da dama dake ci gaba da samun bunkasa a kasar. Ga misali, kamfanoni irin su General Motors, Ford, da Boeing duk suna da hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin, da ke kera motoci da na’urorin jiragen sama a biranen Shanghai da Chengdu.
Har ila yau, ga irin su Apple, Microsoft, da Google da duk sun samu gindin zama a kasar Sin tare da bude ofisoshi da ressan masana’antu a biranen Shanghai, Beijing, da Shenzhen.
Haka nan sauran kamfanoni irin su Coca-Cola, da PepsiCo duk sun tsayu da kafafunsu sosai a kasar. Bugu da kari, ga kamfanonin harkokin biyan kudi ta fasahar zamani kamarsu Amazon da PayPal da su ma suka samu hadin kan kamfanonin kasar Sin don fadada kasuwancinsu a cikin kasar.
Duka wannan yana nuna yadda Sin ke fada da cikawa ne a kan manufofinta na kara bude kofa ga duniya. Kuma ya dace Amurka ta nuna sanin ya kamata a kan bahaguwar fahimtarta da sake lale kan matakanta na haddasa fitina a bangaren kasuwancin duniya.
Sannan ko da za ta nace a kan tana da ikon kara haraji a kan kayayyakin da ake shigo da su kasarta, to ta sani, ita ma tana da kamfanoni a kasashen waje da aka yi masu riga da wando, kuma masu karin magana sun ce, “ana barin halal don kunya!” (Abdulrazaq Yahuza Jere)