Cibiyar bincike kan fasahar sadarwa ta kasar Sin (CAICT), ta bayyana a yau Juma’a cewa, adadin wayar salula da Sin ta samar ya karu da kaso 22.1 a watan Disamban bara, zuwa kusan guda miliyan 34.53.
Cibiyar wadda ke karkashin ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, ta ce zuwa watan Disamban, wayoyi masu sadarwar 5G ne suka dauki kaso 88.1 na adadin, inda jimilarsu ta kama miliyan 30.43, karuwar kaso 25.8 a kan na makamancin lokacin a shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)