Kasar Sin ta sake nanata gargadi a jiya, bayan sanarwar da Amurka da Japan da Korea ta kudu suka fitar yayin taron tsaro na Munich, suna masu bayyana goyon baya ga shigar Taiwan cikin kungiyoyin kasa da kasa?
Abun tambayar a nan shi ne, shin Taiwan ’yantacciyar kasa ce?
Abun kunya ne yadda Amurka ke amai ta na lashewa don gane da batutuwan da suka shafi Taiwan da ma alakarta da kasar Sin a matsayinta na kasar dake ganin kanta babba. Ta ce ba ta goyi bayan ’yancin Taiwan, amma wani sako take aikewa ga ’yan aware yankin? Tabbbas tambayar da za ta kasance cikin zukatan al’ummar duniya ita ce, shin za a iya aminta da kalaman Amurka kuwa?
Batun da ya shafi duk wani yanki na kasar Sin, to batu ne na cikin gidan wanda Sin ce kadai ke da hakki da ikon yanke hukunci a kai. Amurka da kawayenta cikin sanarwar da suka fitar sun nanata goyon bayansu ga wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Taiwan. Sai dai, duk wanda ke bibiyar harkokin duniya, ya san ire-iren kamalan Amurka, su ne ke barazana ga zaman lafiyar yankin. Tana amfani da yankin wajen takalar Sin da kokarin dakile ta, sai dai, idan rana ta fito, tafin hannu bai iya kare ta. Kasar Sin ta riga ta samu ci gaba, kuma tana da dabarun tabbatar da dorewar nasarorinta, don haka babu wani abu da Amurka da kawayenta za su yi da zai durkusar da kasar. Kazalika, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakan da suka wajaba na kare cikakken ’yancinta, ta yi kuma an gani a yankin Hong Kong a shekarun baya.
Yanzu haka kokari ake yi na ganin an shawo kan rikice-rikicen da duniya ke fama da su, amma Amurka da kawayenta kokari suke yi su ci gaba da haifar da hargitsi. Kamar yadda kowa ya sani, kyakkyawar dangantaka tsakanin Sin da Amurka za ta samar da dimbin alfanu ga duniya, don haka, ya kamata Amurka ta yi karatun ta nutsu, kada ta lalata ragowar dangantakar dake tsakaninta da Sin, maimakon haka ta hada hannu da ita, su ceto duniya daga halin take ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp