Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya kaddamar da rabon awaki 40,000 ga mata 3,610 domin habaka kiwo da bunkasa tattalin arziki.
Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da wani shiri a garin dankola da ke karamar hukumar Daura, Gwamna Radda ya ce an yi haka ne domin a tallafa wa mata masu kananan sana’o’i a fadin Jihar Katsina.
- Hisbah Ta Haramta Gidajen Casun Dare A Katsina
- Da Dama Sun Rasu Yayin Da NAF Ta Kai Wa ‘Yan Bindiga Hari A Katsina
Haka kuma ya yi karin haske kan wannan shiri na rabon awaki wanda ya ce gwamnatinsa na da kudirin bunkasa harkar kiwo wanda arewacin Nigeriya ya kware da shi tun asali, kuma hanya ce ta bunkasa tattalin arziki cikin sauki.
Gwamna Radda ya ce mata su ne kan gaba wajen ganin an tallafa masu ta hanyar ma’aikatar harkokin mata da kuma matakin al’umma.
“Samar da wadannan awaki ya lakume kudi naira na gogar naira har naira biliyan 5.7, domin kawai a tallafa wa mata ta hanyar ba su jarin kiwo domin samun nasarar su,” in ji shi.
Gwamnan ya gargadi jami’an gwamnati da su kauce wa dabi’ar nuna san kai da rashin gaskiya wajen zabo matan da za su amfana da wannan tallafi.
A cewar Gwamna Radda, an zabo mata 10 daga kowace guduma, kuma za a bai wa kowace mace awaki guda hudu da suka hada awaki uku da bunsuru daya, sannan za a bai wa kwararren manomi guda hamsin wanda zai koyar da su dubarun kiwo.
Tun da farko da take jawabi, kwaminisiyar harkokin mata ta Jihar Katsina, Hajiya Hadiza Yar’adua ta bayyana wannan tallafi a matsayin wata gagarumar gudummawa da gwamnati za ta bunkasa harkokin mata ta hanyar dogoro da kai.
A cewarta, taimakon da Gwamna Radda ya bayar ko shakka babu zai amfani mata masu sana’o’i tare bunkasa tattalin arziki a Jihar Katsina da ƙasa baki daya.