Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da aiwatar da matakin buga harajin kwastam daidai-wa-daida tsakanin Amurka da sauran kasashe, ba da dadewa ba da ya buga karin haraji na kashi 25% kan kayayyakin karfe da goran ruwa da ake shigowa da su kasar. Abubuwa ba su zo da mamaki ba duba da cewa, Trump ya sha amfani da makamin harajin kwastam don tabbatar da cewa, muradun Amurka na gaba da komai.
Ba shakka, matakin da Amurka ke dauka na keta tsarin ka’idojin cinikin duniya. Babban jami’i mai kula da harkar tattalin arziki na EU Valdis Dombrovskis ya bayyana a kwanan baya cewa, rashin tabbas da shirin kara wa Turai haraji ya haifar, ya kawo cikas ga shigowar jari a kasashen Turai, abin da ya kawo mumunan tasiri. Jaridar Wall Street ta Amurka ta yi nazarci cewa, matakin buga harajin kwastam na daidai-wa-daida tsakaninta da sauran kasashe da Amurka ta yi zai kara jefa kasashe masu tasowa cikin wahalhalu, musamman ma Indiya da Brazil da Vietnam da Argentina da dai sauran kasashen kudu maso gabashin Asiya da ma kasashen Afirka.
Matakin ba kawo cikas ga kasashen duniya kadai ya yi ba, har ma zai illata Amurka ita kanta, sakamakon yadda shirinta na sanya karin haraji ya haifar da damuwar hauhawar farashi a cikin gidan Amurka. Kafar yada labarai ta Reuters ta ba da labari cewa, yawancin masanan tattalin arziki na ganin cewa, karin haraji zai haifar da hauhawar farashi da rasa guraben aikin yi.
Matakin harajin da Amurka ta dauka ya keta tsarin gudanar da ciniki tsakanin mabanbantan bangarori da dokokin WTO. Mai da moriyar Amurka a gaban komai zai keta tsarin tattalin arziki da cinikin duniya. Abokan cinikin Amurka ba shakka za su mai da martani, abin da zai haifar da karin mumunan tasiri, kuma zai tsananatar da kariyar ciniki da wargaza tsarin samar da kayayyaki a duniya. (Mai zane da rubutu: MINA)