Bayan da kasar Amurka ta dakatar da ba da tallafi, kafofin watsa labaru na Najeriya da sauran kasashe dake nahiyar Afirka sun bayyana damuwa kan karancin kudin gudanar da ayyukan kiwon lafiya a kasashensu, da nuna takaici kan yadda gwamnatin kasar Amurka ta dauki mataki ba tare da lura da nauyin dake wuyanta ba. Sai dai idan mu duba kewayenmu, to, za mu ga ashe ba mutanen Afirka kadai ke nuna damuwa da takaici a wannan karo ba.
A nahiyar Turai, kasar Amurka ta yi wa tsoffin kawayenta kasashen Turai kakkausan suka, sa’an nan ta fara shawarwari da kasar Rasha su biyu kadai, lamarin da ya zama juya baya ga kasashen kungiyar EU da Ukraine, ganin yadda wadannan kasashe suka taka muhimmiyar rawa a yakin Rasha da Ukraine, karkashin jagorancin kasar Amurka din.
- Ƴansanda Sun Kama Ɓarayin Waya Masu Amfani Da Keke Napep A Adamawa
- Ƴansanda Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga Kan Jami’an NSCDC A Katsina
A nahiyar Amurka kuma, kasar Amurka ta ce za ta mamaye kasar Canada, da neman mallakar koramar Panama, da tsibirin Greenland, ta yadda ta sanya makwabtanta da dama karkashin barazanar kwace yankunansu.
Kana a nahiyar Asiya, Amurka ta ce za ta karbi ikon mulkin yankin Gaza, da korar Falasdinawa daga yankin, maganar da ta fusata dimbin kasashe masu bin addinin Islama.
Haka zalika, ta hanyar kaddamar da yakin harajin kwastam, kasar Amurka ta lahanta moriyar kasashen Canada, da Mexico, da Sin, da Jamus, da dai sauransu.
To, ma iya cewa kasar Amurka ta riga ta fusata dukkan kasashen duniya. Idan an sa wata kasar dake nahiyar Afirka fuskantar matakin da kasar Amurka ta dauka ita kadai, to, za ta ji akwai matsin lamba. Sai dai yanzu za a saki jiki, saboda ko da yake kasar Amurka ta kan ci zarafin sauran kasashe, amma ba ta da karfin cin zarafin dukkan kasashe a sa’i daya. Wannan shi ne dalilin da ya sa ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a wajen taron aikin tsaro na Munich da ya gudana a kwanan nan, cewa bai kamata a ji tsoron aikace-aikacen kasar da ta ke ta nuna fin karfi a duniya ba, saboda galibin kasashen duniya dake tsayawa kan adalci da hadin kai za su cimma nasara a karshe.
Ban da halartar taron tsaro a Munich a wannan karo, Wang Yi ya kuma shugabanci taron kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, da halartar taron ministocin waje na rukunin kasashe 20 (G20), duk a kwanakin baya. Inda ya jaddada manufofin Sin na aiwatar da ra’ayin kasancewar bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya, da tsayawa kan daidaituwa, da adalci, da hadin kai, gami da neman zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna, da dai sauransu. Mahalarta tarukan sun nuna yabo kan jawaban ministan na kasar Sin, ganin yadda maganarsa ta kwantar da hankalinsu. Saboda ta nuna cewa, kasar Sin har kullum tana samar da tabbaci ga tsare-tsaren duniya, da ba da gudunmowa a kokarin tabbatar da ci gaban harkokin duniya.
Ban da haka, Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Angola, dake shugabantar kungiyar kasashen Afirka ta AU a karba-karba, Tete Antonio. Inda Wang ya ce, “‘Yan uwa Sinawa dake nahiyar Afirka sun san wace ce kawa ta gaske ta Afirka. “Wannan wata tsohuwar magana ce, amma yanzu ta nuna ma’ana mai zurfi.
Haka zalika, Wang ya ce, “A yunkurin kasashen Afirka na raya kai a nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin ba da taimako a matsayin wata sahihiyar abokiya.” Tabbas, za a iya tabbatar da makomar Afirka mai haske, bisa hadin kanta da kasar Sin, da huldar cude-ni-in-cude-ka dake tsakanin daukacin kasashe masu tasowa. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp