Ministar harkokin wajen Madagascar Rasata Rafaravavitafika ta bayyana a Tananarive, hedkwatar kasar jiya Litinin cewa, ana godiya ga Sin da ta dade take tura tawagogin likitanci zuwa kasar cikin shekaru 50 da suka gabata, don ba da tallafin jinya na zamani a yankuna masu nisa na Madagascar, da ceton rayuka na miliyoyin mutane dake wuraren.
Rasata ta bayyana hakan ne yayin halartar bikin sa hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar tawagogin likitanci ta Sin tsakanin Sin da Madagascar.
Ji Ping, jakadan Sin dake Madagascar da Randriamanantany Zelyarivelo, ministan kiwon lafiyar jama’a na Madagascar, suka sa hannu a kan yarjejeniyar. (Safiyah Ma)