Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta tsakiya, za ta fuskanci kwamitin da’a na majalisar dattawa, biyo bayan samun sabani da ta samu tsakaninta da shugaban majalisar dattijai, Akpabio.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya sanar da matakin a zaman majalisar na ranar Talata, inda ya bayyana cewa an mika batun a hukumance don sake duba lamarin.
- Darajar Naira Ta Farfaɗo A Kasuwar Hada-Hadar Kuɗi Ta Duniya
- LEADERSHIP HAUSA Ta Bayyana Waɗanda Suka Yi Nasara A Gasar Gajerun Labaran Soyayya
Akpabio ya jaddada cewa kwamitin ladabtarwa zai binciki lamarin tare da kai rahoto ga majalisar dattawa domin daukar mataki.
Sakamakon binciken da kwamitin ya yi, zai tantance matakin da za a dauka na gaba.