Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Attahiru Jega, ya yi gargadin cewa tasirin dimokuradiyya a Afirka ta Yamma na raguwa saboda rashin shugabanci nagari.
Da yake jawabi a Abuja ranar Talata a matsayin babban mai jawabi a wani taro mai taken, “Mahanga kan makomar zabe a Afirka ta yamma”, wanda wata kungiyar al’umma ta ‘Yiaga Africa’ ta shirya, ya danganta komowar juyin mulkin soji a yankin da rashin shugabanci nagari.
- An Gudanar Da Taron Dandalin Ciniki Tsakanin Sin Da Habasha A Addis Ababa
- Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa
Ya yi nuni da juyin mulkin baya-bayan nan da aka yi a Mali, Burkina Faso, Guinea, da Nijar, a matsayin alamu karara na nuna rashin gamsuwa da tsarin mulkin shugabannin yankin, inda ya zarge su da fifita bukatun kashin kai fiye da bukatun ‘yan kasarsu.
“Waɗanda ake kira zaɓaɓɓun wakilan jama’a sun mayar da dukiyar jama’a zuwa ga bukatun kashin kansu,” in ji shi.
Jega ya yi zargin cewa, koma bayan dimokuradiyya da gazawar gwamnati ke haifarwa ne ya bai wa sojoji damar juyin mulki, wanda ke kawo barazana ga zaman lafiyar yankin.
Ya kuma soki shugabannin siyasa da yin magudin zabe domin ci gaba da rike madafun iko maimakon karfafa dimokuradiyya.
“Zabuka sun zama wata hanya kawai ta tafka magudi don bai wa shugabannin da ke kan kujerar mulki ci gaba da rike madafun iko,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp