• English
  • Business News
Friday, June 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwan Da Suka Ta Da Kura A Litttafin Janar Babangida

by Sani Anwar
3 months ago
in Manyan Labarai
0
Abubuwan Da Suka Ta Da Kura A Litttafin Janar Babangida
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A ranar Alhamis, 20 ga watan Fabrairun 2025 ne, tsoffin shugabannin Nijeriya da na kasashe masu makwabtaka da ita, da sauran masu fada a ji, suka hallara wajen kaddamar da littafin tarihin Shugaban Mulkin Sojan Nijeriya; Janar Ibrahim Badamasi Babangida, mai suna ‘A Journey In Serbice’, a Abuja.

Bikin ya samu halartar tsoffin shugabannin Nijeriya da suka hada da Janar Yakubu Gawan, Janar Olusegun Obasanjo, Janar Abdussalami Abubakar, Goodluck Ibele Jonathan da kuma tsoffin shugabannin kasar Ghana, Nana Akufo Addo da na Kasar Sierra Leone, Arnest Bai Koroma.

  • Hukuma Ta Rufe Gidajen Gala A Jihar Kano
  • Gwamnatin Kano Za Ta Ɗau Nauyin Ɗalibai 1,002 Domin Karatu A Ƙasashen Waje

Littafin mai shafi 400, ya yi waiwaye kan rayuwar tsohon shugaban kasar daga yarintarsa a matsayinsa na maraya zuwa gwagwarmayar karatunsa da kuma aikin soja.

Kaddamar da littafin, ya yi matukar tayar da kura, musamman idan aka yi la’akari da abubuwan da ke kunshe a cikinsa da kuma wadanda suka biyo bayan kaddamarwar a kafafen yada labarai da sauran shafukan sada zumunta na kasar nan.

Tsohon shugaban mulkin sojan, ya bayyana marigayi Cif Moshood Abiola, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993, a cikin littafin nasa.

Labarai Masu Nasaba

Ba Zan Bar Nijeriya Ta Zama Kasa Mai Jam’iyya Daya Ba – Tinubu

Sojoji Sun Kashe Auta, Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda Da Wasu 13 a Jihar Zamfara

Har ila yau, a cewarsa; Abiola ya samu mafi yawan kuri’u tare da cika dukkanin sharudan da ake bukata, domin zama shugaban kasa. “Babu tantama a zuciyata, Abiola ne ya lashe wannan zabe tare da cika dukkanin sharudan da ake bukata”, in ji IBB.

Kazalika, ya kuma bayyana farin cikinsa; kan yadda Buhari ya karrama Abiola da lambar yabo mafi girma ta GCFR, wadda ake bai wa shugabannin kasa.

“Ko shakka babu, Mashood Abiola shi ne ya lashe zaben shugaban kasa a 1993, da kuri’u sama da miliyan takwas a jam’iyyasa ta SDP, inda ya samu nasara a kan abokin karawarsa, Alhaji Bashir Othman Tofa na jam’iyyar NRC”, in ji Babangida.

A jawabinsa na godiya, IBB ya bayyana rushe zaben 1993 a matsayin wani abu da ya yi yake kuma da-na-sanin yin sa a rayuwarsa.

Har ila yau, Janar Babangida a cikin littafin nasa, ya bayyana dalilinsa na kifar da gwamnatin Buhari, duk kuwa da cewa; shi ne babban hafsan sojin kasar a 1985.

Guda daga cikin dalilan nasa su ne, a babi na shida ya bayar da hujjar cewa; juyin mulkin, wani martani ne ga korafe-korafen ‘yan Nijeriya na bakar azaba da wahalar da suka sha da kuma tabarbarewar al’amuran kasar baki-daya.

“A farkon shekarar 1985, ‘yan Nijeriya sun fara fargaba game da makomar kasarmu, wanda al’amuran suka kasance a matsayin masu matukar hadari, wanda kuma hakan yanzu ma alamu ne a fili na irin wancan hatsari.

“Babu shakka, a bayyane yake ga shugabancin sojoji cewa, aikin da muka yi da nufin ceto kasarmu a shekarar 1983 ya tarwatshe”, kamar yadda ya rubuta a littafin.

Ya kara da cewa, rashin daukar mataki zai iya kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin sojoji, wanda a ganinsa; hakan kan iya haifar da mummunar illa ga kasar.

“Idan sojoji suka samu rarrabuwar kai, al’ummar kasa za su bi sahunsu; sannan abin da zai biyo baya na iya kasancewa mai matukar ban tsoro da ba a taba tunani ba”, a cewarsa.

IBB, ya ci gaba da bayyana cewa, a shekarar 1983; sojoji sun hambarar da gwamnatin Shehu Shagari ne cikin hadin kai, amma sai aka fara samun rarrabuwar kawuna a tsakaninsu daga bisani.

“A matsayin sojoji na wadanda aka sani da hadin kai, sai ga shi kuma an fara samun guna-guni a tsakaninsu, wannan ne yasa dole a yi wani abu, don gudun kada mu rasa kasar”.

Babangida ya ce, “Babban abin da na ji tsoro shi ne, samun rarrabuwar kawuna da ra’ayoyi a tsakanin sojoji na iya haifar da bangaranci a tsakaninsu, wanda idan kuma aka bari abin ya ci gaba da samun gindin zama, akwai hatsarin gaske”.

Haka zalika, ya zargi Buhari da mataimakinsa Birgediya Janar Tunde Idiagbon da mayar da sojoji saniyar ware tare kuma da daukar tsauraran matakan kama-karya wajen tafiyar da mulki.

A cewar tasa, gwamnatin Buhari ta yi mulki ta hanyar tsoratarwa, maimakon sanya kyawawan fata a zukatan al’umma.

“Kyautuwa ya yi mu inganta rayuwarsu, mu karfafa musu gwiwa, don ganin rayuwar tasu ta inganta. Maimakon haka, sai aka yi ta faman kafa musu dokokin kama-karya. Wannan dalili ne yasa, aka wayi gari gwamnatin da aka kafa da niyyar cimma muradun bai-daya na sojoji, ta koma ta wasu ‘yan tsirarun mutane masu taurin kai”, in ji Babangida.

Ya bayyana cewa, “Yawancin juyin mulkin soja, muna yi ne sakamakon yawan korafe-korafen al’umma, musamman Talakawan da suka shiga matsanancin halin rayuwa, sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da aka yi ta faman fuskanta na yau da kullum”.

“Haka zalika, batun komawa amfani da tsohuwar hanyar aiwatar da musayar kayayyaki a kasuwanci na kasa da kasa, na nufin cewa; kwata-kwata ba a kama hanyar kawo karshen matsalolin tattalin arzikin a tsakanin al’umma ba”, in ji IBB.

Har wa yau, sanin kowa ne cewa; dokokin kama-karya, sun tauye ‘yancin walwalar jama’a kai tsaye, sannan kuma ga hukunci mai tsauri, kamar yadda ya bayyana a littafin.

Kazalika, kayayyakin masarufi da sauran bukatun yau da kullum, sun yi matukar karanci, duk dai a wancan lokaci na mulki Buhari, in ji Babangida.

A bangare guda kuma, Janar Babangida a cikin littafin nasa, ya zargi marigayi tsohon shugaban kasa; Janar Sani Abacha da laifin yunkurin kifar da gwamnatinsa ta karfi da yaji da kuma zargin laifin soke zaben shugaban kasa na shekarar 1993.

Badamasi, ya amince da aikata babban kuskure a lokacin da yake shugabancin Najeriya, na gaza yi wa Sani Abacha ritaya daga aikin soja.

A lokacin, Abacha shi ne babban hasfan tsaro; wanda ya kwace mulki tsawon wata uku, bayan Babangida ya ajiye mukaminsa na shugabancin kasa.

Babangida ya kara da cewa, duk da shi da Abacha abokan juna ne, amma a fili yake cewa; Abacha mutum ne mai wuyar sha’ani, wanda ke biye wa munanan zantukan da ke faruwa a tsakanin rundunar sojin Nijeriya.

“Na yi mamakin yadda shi da wasu mutane suke da mummunar fahimta a kaina tare da nuna cewa, ni ne matsala,” in ji Babangida”.

A cikin littafin nasa ya ce, Abacha ne ya kitsa yadda za a cire shi daga shugaban kasa. Sai dai duk da haka, bai sallame shi daga aikin soja ba, saboda gudun zubar da jini a cikin rundunar sojin.

“A lokacin kan jami’an rundunar soji a rarrabe yake, don haka; duk wani yunkuri a lokacin, ka iya haifar da mummunar matsala,” in ji Babangida.

“Abin ya kai ga idan na yi wani kuskure daga bangarena, zai iya jawo zubar da jini, saboda za a samu yunkurin yin juyin mulki.”

Wannan tsokaci da IBB ya yi a littafin nasa, ya ja hankalin iyalan marigayi Sani Abacha, da ta kai har guda daga cikin ‘ya’yansa; Sadik Abacha ya mayar masa da martanin cewa, ‘yan Nijeriya ba za su taba mantawa da kokarin da mahaifinsu ya yi a bangaren ci gaban kasa ba, sannan kuma za su ci gaba da yaba masa kamar yadda suka saba.

“Mahaifina Abacha, kai ne a koda-yaushe suke yi maka hassada da bakin ciki. Saboda haka, tarihi zai ci gaba da tunawa da kai a matsayin shugaba nagari, ko su yabe ka; ko su yi suka, a matsayina na da, ina alfahari da kai, domin kuwa dukkaninsu suna fatan kai wa rabin matsayinka”, in ji Sadik.

Bugu da kari, makudan kudaden da aka tara a wajen kaddamar da littafin, ya yi matukar jawo cece-kuce a tsakanin ‘yan Nijeriya, domin kuwa Naira na gugar Naira har biliyan 17.5 aka tara wa tsohon shugaban kasar; don gina dakin karatu.

Har ila yau, Alhaji Aliko Dangote, Abdussamad Rabi’u, Janar TY Danjuma, Arthur Eze da sauran makamantansu, su ne wadanda suka tara wadannan makudan kudade; a matsayin gudunmawa, domin gina wannan katafaren dakin karatu na Janar Babangida.

Wanda ya fi kowa tarin dukiya a dukkanin fadin Afirka, Aliko Dangote, ya bayar da gudunmawar Naira biliyan biyu tare kuma da alkawarin ci gaba da bayar Naira biliyan biyu-biyu tsawon shekara uku, wanda idan aka hada jimillarsu zai kama Naira biliyan takwas.

Sai kuma Alhaji Abdussamad Rabi’u, wanda ya bayar da Naira biliyan biyar; duk da cewa, IBB ya bayyana cewa; tuni ya fara bayar da tasa gudunmawar wajen ginin wannan daki na karatu.

Akwai kuma, tsohon hafsan soji kuma ministan tsaro; TY Danjuma da ya yi alkawarin bayar da Naira biliyan uku. Sai wani shahararren Dan kasuwa mai suna Arthur Eze, shi ma ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 500.

Haka nan, akwai wasu da dama su ma da suka bayar da wannan gudunmawa da kuma wadanda suka yi alkawari; duk dai a wajen wannan kaddamar da katafaren littafi na Janar Ibrahim Badamasi Babangida.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: BabangidaIBBKuraLittafi
ShareTweetSendShare
Previous Post

Yadda Matasa Ke Kara Shiga Harkar Tsaface-tsaface

Next Post

LEADERSHIP HAUSA Ta Bayyana Wadanda Suka Yi Nasara A Gasar Gajerun Labaran Soyayya

Related

Ba Zan Bar Nijeriya Ta Zama Kasa Mai Jam’iyya Daya Ba – Tinubu
Manyan Labarai

Ba Zan Bar Nijeriya Ta Zama Kasa Mai Jam’iyya Daya Ba – Tinubu

7 hours ago
Sojoji Sun Kashe Auta, Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda Da Wasu 13 a Jihar Zamfara
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Auta, Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda Da Wasu 13 a Jihar Zamfara

9 hours ago
Zamfara: APC Za Ta Maka PDP A Kotu Kan Zargin Matawalle Da Hannu A Satar Mutane
Manyan Labarai

Zamfara: APC Za Ta Maka PDP A Kotu Kan Zargin Matawalle Da Hannu A Satar Mutane

12 hours ago
EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Zargi Aikata Damfara A Intanet A Kaduna
Manyan Labarai

EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Zargi Aikata Damfara A Intanet A Kaduna

13 hours ago
Zan Ci Gaba Da Ɓata Wa Masu Sukar Tinubu Rai Da Ayyuka – Wike
Manyan Labarai

Zan Ci Gaba Da Ɓata Wa Masu Sukar Tinubu Rai Da Ayyuka – Wike

17 hours ago
Duk Da Cewa Wike Ba Ɗan APC Ba Ne Amma Muna Jin Daɗin Aikin sa – Tinubu
Manyan Labarai

Duk Da Cewa Wike Ba Ɗan APC Ba Ne Amma Muna Jin Daɗin Aikin sa – Tinubu

1 day ago
Next Post
LEADERSHIP HAUSA Ta Bayyana Wadanda Suka Yi Nasara A Gasar Gajerun Labaran Soyayya

LEADERSHIP HAUSA Ta Bayyana Wadanda Suka Yi Nasara A Gasar Gajerun Labaran Soyayya

LABARAI MASU NASABA

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: An Yi Kira Ga Amurka Da Ta Cimma Daidaito Da Sin Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: An Yi Kira Ga Amurka Da Ta Cimma Daidaito Da Sin Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya

June 12, 2025
Ba Zan Bar Nijeriya Ta Zama Kasa Mai Jam’iyya Daya Ba – Tinubu

Cikakken Jerin Sunaye: Tinubu Ya Karrama ‘Yan Nijeriya 102 Don Bukin Ranar Dimokuradiyya Ta 2025

June 12, 2025
Sin Na Fatan Amurka Ta Yi Hadin Gwiwa Da Ita Don Tabbatar Da Matsayar Da Shugabannin Kasashen Biyu Suka Cimma

Sin Na Fatan Amurka Ta Yi Hadin Gwiwa Da Ita Don Tabbatar Da Matsayar Da Shugabannin Kasashen Biyu Suka Cimma

June 12, 2025
Sin Ta sanya Indonesiya Cikin Tsarin Shiga Kasar Ba Tare Da Biza Ba Na Sa’o’i 240 Da Kara Yawan Kasashen Tsarin Zuwa 55

Sin Ta sanya Indonesiya Cikin Tsarin Shiga Kasar Ba Tare Da Biza Ba Na Sa’o’i 240 Da Kara Yawan Kasashen Tsarin Zuwa 55

June 12, 2025
Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka

Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka

June 12, 2025
Zambar Naira Miliyan 55: ICPC Ta Fara Bin Diddigin Dan Kwangilar Dam Din Jihar Filato

ICPC Ta Gurfanar Da Ma’aikacin Kotu Bisa Badakalar Naira Miliyan 9.2

June 12, 2025
Fahimtar Sabon Tunani: Raya Kimiyya Da Fasaha Da Dogaro Da Karfi Na Kashin Kai Sun Ingiza Ci Gaban Kasar Sin 

Fahimtar Sabon Tunani: Raya Kimiyya Da Fasaha Da Dogaro Da Karfi Na Kashin Kai Sun Ingiza Ci Gaban Kasar Sin 

June 12, 2025
De Bruyne Ya Kammala Komawa Napoli Bayan Barin Man City

De Bruyne Ya Kammala Komawa Napoli Bayan Barin Man City

June 12, 2025
Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa: Sabon Tunani Don Wanzar Da Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya

Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa: Sabon Tunani Don Wanzar Da Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya

June 12, 2025
Ba Zan Bar Nijeriya Ta Zama Kasa Mai Jam’iyya Daya Ba – Tinubu

Ba Zan Bar Nijeriya Ta Zama Kasa Mai Jam’iyya Daya Ba – Tinubu

June 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.