Bisa labarin da shafin intanet na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC ya fitar, za a gudanar da taron manema labarai na taro na uku na NPC karo na 14, a zauren taron manema labarai na babban dakin taron jama’a, da karfe 12 na safiyar ranar 4 ga watan Maris, inda mai magana da yawun taron zai amsa tambayoyi daga ‘yan jaridun kasar Sin da na kasashen waje kan batutuwan da suka shafi ajandar taron da kuma ayyukan NPC.
Shafin ya kuma bayyana cewa, ana maraba da ‘yan jaridun kasar Sin da na kasashen waje su halarci taron na manema labarai. (Safiyah Ma)