Hukumar kula da gandun daji da filayen ciyayi ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, namun dajin kasar ta Sin sun karu yadda ya kamata ba tare da cikas ba.
Adadin manyan dabbobin Panda ya karu daga kimanin 1,100 a shekarun 1980 zuwa kusan 1,900 a yau, yayin da yawan damisar dusar kankara ya kai fiye da 1,200. Sai kuma adadin giwayen daji nau’in na Asiya da ya karu daga fiye da 150 zuwa sama da 300.
A fannin shuke-shuke da tsirrai na daji kuwa, an samu nasarar dawo da nau’o’in halittunsu fiye da 200 dake cikin hadarin bacewa bat a duniya, kuma yawancin jinsunansu sun farfado tare da samun kariya yadda ya kamata.
Yau Litinin ne ake tunawa da ranar kare namun daji ta duniya ta shekarar 2025 wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp