Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umarnin dakatar da taimakon da Amurka ke bai wa Ukraine, a yunkurin shugaban na tursasa shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy karbar yarjejeniyar sulhu don kawo karshen yaki da Rasha.
Wannan na zuwa ne bayan Trump ya caccaki Zelenskyy saboda rashin nuna godiya ga goyon bayan Amurka ke bai wa kasarsa.
- Kakaki: A Ko Da Yaushe Kasar Sin Tana Tsayawa Tare Da Kasashe Masu Tasowa
- Ba Za Mu Tattauna da Rasha Ba Sai Ta Daina Kai Mana Hari – Zelensky
“Shugaba Trump ya bayyana karara cewa, ya mai da hankali kan tabbatar da zaman lafiya. Don haka, abokan hulɗar mu dole su jajirce kan cika wannan burin su ma.” in ji wani jami’in Amurka.
Sai dai, Firaministan Ukraine Denys Shmyhal ya ce, har yanzu Kyiv na da isassun makamai da za ta kai wa dakarunta dake yaki a gaba-gaba.
“Taimakon kayayyakin Soji na Amurka yana da mahimmanci kuma yana ceton dubban rayuka, don haka, Kyiv za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta ci gaba da alaka da Washington”. In ji Shmyhal
Shmyhal ya kara shaida cewa, “Muna da mafita ɗaya kawai – nasara don tsira. Ko dai mu ci nasara, ko kuma wani ya rubuta mana shiri na biyu.”
A nata bangaren, fadar Kremlin ta Rasha ta ce, katse tallafin soji ga Ukraine shi ne matakin da ya fi dacewa don samar da zaman lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp