A yau Talata, kasar Sin ta bakin ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar ta bayyana rashin jin dadinta game da karin harajin da Amurka ta yi ikirarin sanyawa kayayyakin kasar, bisa kafa hujja da maganin Fentanyl.
Kamar yadda kakakin ma’aikatar ya bayyana, Sin tana daya daga cikin kasashe mafiya tsauraran matakan yaki da miyagun kwayoyi ko sarrafa su. Tabbas kasar Sin kasa ce mai sa ido da daukar tsauraran matakan dakilewa da yaki da tu’ammali da duk wani abu mai illa, musammam miyagun kwayoyi, kuma tana iyakar kokarinta kan wannan batu. Idan ba a manta ba, kasar Sin ce ta jagoranci duniya wajen tsara jerin rukunin kwayoyin Fentanyl da sauran abubuwan da suka jibance shi a watan Mayun 2019, inda ta taka muhimmiyar rawa wajen hana samarwa da safara da kuma amfani da shi. Baya ga haka, tana iyakar kokarinta wajen hada gwiwa da taimakawa Amurka don shawo kan batun.
- Kakaki: A Ko Da Yaushe Kasar Sin Tana Tsayawa Tare Da Kasashe Masu Tasowa
- Za A Sake Gurfanar da Blatter Da Platini Kan Zargin Cin Hanci
Sai dai, duk da wannan kokari da Sin take yi, har yanzu Amurka na kafa hujja da batun wajen kakaba takunkumin ba gaira ba dalili da kuma kakaba haraji duk da cewa, kasashen biyu sun yi tattaunawa mai zurfi tare da hada hannu kan batun dakile tu’ammali da Fentanyl, kuma an samu kyawawan sakamako.
Akwai bukatar Amurka ta gane cewa, rikici da fito na fito ba zai taba kawo ci gaban da take nema ba. Haka kuma, yakin haraji da cinikayya, tsaiko zai kawo tare da mayar da hannun agogo baya don gane da nasarori da sakamakon da aka samu wajen dakile Fentanyl din da ma dangantakar dake tsakaninta da Sin. Bugu da kari, ya kamata Amurka ta rika kokarin lalubo inda take da matsaloli ta kuma gyara su, maimakon har kullum ta kasance mai dorawa wasu laifi. Kaucewa daukar nauyin matsalolinta da shawo kan su, ba zai taba kawo mata mafita ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp