A yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda a yayin taron, wani dan jarida ya gabatar da tambaya game da matakin Amurka, na sake kakabawa Sin karin harajin kashi 10 cikin dari, bisa fakewa da batun sinadarin kashe radadi na Fentanyl. Game da hakan, Lin Jian ya bayyana cewa, bangaren Sin ya riga ya sha fayyace matsayinsa na nuna adawa da matakin.
Ya ce, har kullum jama’ar kasar Sin suna adawa da nuna fin karfi, da yin matsin lamba, da tilastawa, da kuma barazana, saboda hakan ba hanya ce da ta dace a bi yayin mu’ammala da kasar Sin ba.
Ya kara da cewa, idan bangaren Amurka yana son warware batun Fentanly, ya kamata ya tattauna tare da bangaren Sin bisa daidaito, da mutunta juna, da samun moriyar juna, har a kai ga warware matsalolin dake tsakani. To amma idan har Amurka na da wasu manufofi, kuma ta nace a kan kaddamar da yakin haraji, da yakin kasuwanci ko wani yaki na daban, kasar Sin za ta tunkari yakin har zuwa karshe.(Safiyah Ma)














