Majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14, wadda ita ce majalisar dokokin kasar Sin, ta gudanar da taron rufe zaman babban taronta a yau Talata. Shugaba Xi Jinping tare da sauran jagororin gwamnatin kasar sun halarci taron, wanda ya gudana a katafaren zauren taron jama’ar kasar Sin, wato “Great Hall of the People” da ke birnin Beijing.
A dai yau din, majalissar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, ta zartar da rahoton aikin gwamnati, da rahoton aikin zaunannen kwamitin majalissar ta NPC, da rahoton aiki na kotun kolin al’ummar kasa, da rahoton aikin hukumar koli ta gabatar da kara. Kazalika, taron ya amince da shirin yara tattalin arziki, da bunkasa zamantakewar al’ummar kasa na shekarar 2025, da babban kasafin kudi na shekarar ta 2025.
Bugu da kari, taron ya zartar da dokar aikin wakilan jama’a da aka sabunta yiwa gyaran fuska ta hanyar kada kuri’a, wadda wannan ne karo na 4 da aka yi mata kwaskwarima, tun kafa ta da fara aiwatar da ita a shekarar 1992.
An shigar da tsarin dimokaradiyyar al’umma cikin daukacin aikin a karon farko, ciki har da manyan tanade-tanaden doka. Kari kan haka, an fadada da zurfafa dokar aikin wakilan jama’a da aka sabunta yiwa kwaskwarima, ta yadda ta zamo mai hade sassa biyu na tsarin gudanarwa, wato karfafa hade sassan shugabanci da na jami’an majalissar wakilan jama’ar kasar Sin, da kuma karfafa hade jami’an majalissar wakilan jama’ar kasar Sin da al’ummar kasa. (Masu Fassara: Saminu Alhassan, Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp