- Addini Da Al’ada Da Rashin Kudi Na Yi Mana Tarnaki –Kungiyoyin Mata
- An Samu Karin Mata Masu Rike da Madafun Iko -Bincike
A yau kimamin shekaru 65 kenan da shigar mata a cikin harkokin siyasa a fadin duniya tun bayan samun nasarar Sirima Bandaranalke a matsayin shugabar gwamnatin Sri Lanka a 1960.
A makon jiya ne dimbin mata suka gudanar da ranar mata ta duniya domin kare hakkokin mata da samar da daidaito tsakanin su da takwarorinsu maza.
- Uwargidan Tinubu Ta Bai Wa Mata Manoma Tallafin Naira Miliyan 26 A Nasarawa
- Harajin Da Amurka Ke Kakabawa Na Nuna Dabi’arta Ta Kariyar Cinikayya
Ranar mata ta duniya muhimmiyar rana ce ga jinsin mata iyayen al’umma wadanda a jiya da yau suke sadaukar da lokacin su wajen ci-gaban al’umma a kowane irin fanni.
An fara gudanar da bukin tunawa da ranar mata shekaru 100 da suka gabata domin karfafawa mata kwarin guiwa da kare hakkokin mata da samar da daidaito da takwarorinsu.
Taken taron ranar mata a wannan shekarar 2025 shi ne “Bukatar gaggauta cimma muradin hakkokin mata” wanda take ne da ke nuni da bukatar da ke akwai ta tabbatar da darajar mata da samun nasarar hakkokin su.
Daga kan shugabancin mace ta farko a duniya, dimbin mata sun samu nasarar kafa gwamnatoci a kasashe daban daban kama daga Bigida Finnbogadatir, shugabar kasar Iceland sa Margaret Thatcher da Theresa May a Burtaniiya da Angela Markus a Jamus da Ellen Johnson Sirleaf a Leberiya da Sheikh Hassina a Bangladesh wadanda duka mata ne wadanda gagarumar gudunmuwar da suka bayar ta wuce shurin masaki.
A Nijeriya sha’anin siyasar mata wani babi ne mai zaman kan sa da mata ke kuka da kokawa kan yadda ake nuna masu kyama da kabilanci a dukkanin jam’iyyu tamkar wani jinsi ne ba na mutane ba.
A bayyane yake cewar gagarumar gudunmuwar da mata ke bayarwa a farfajiyar siyasar Nijeriya ta fi gaban a nanata a bisa ga tasiri da kuri’un su ke yi a kowane irin zabe, sai dai anya suna samun adalci?
Yawan adadin da jinsin mata ke da shi da ya zarta na maza ya ba su cikakkiyar damar tabbatar da nasara ko akasin ta ga ‘yan takarar dukkanin mukamai kama daga kansila zuwa shugaban kasa wanda hakan karara ya nuna karfin ikon da mata ke da shi wajen azata ta zauna a siyasar kasar nan.
Mata da yawa sun zama kallabi tsakanin rawuna ta yadda suke zaburar da mutane da dama kan yadda suke sauke nauyin jagorancin da ke kan su da hannu biyu.
Sai dai duk da kima, tasiri da muhimmancin kuri’un mata a zabukan siyasar Nijeriya suna fuskantar dimbin kalubale a dukkanin al’amurran siyasa tamkar ba su da wata muhimmiyar rawar takawa.
Kama daga kan rashin samun goyon baya daga jam’iyyun siyasa, karancin iyayen gida akasin daya jinsin da siyasar ubangida ta mamaye da juya masu baya a kakar zabe da sauransu manyan kalubale ne da mata ke fuskanta.
Matsalolin cin zarafi, camfe- camfen al”ada da batun addini suna matsayin manya- manyan tarin matsalolin da mata suke fuskanta a siyasar jiya kuma suke fuskanta a siyasar yau wadda idan ba wani sauyi aka samu ba haka lamarin zai ci-gaba da kasancewar a siyasar yau da gobe.
Duk da gagarumar muhimmiyar rawar da mata ke takawa a siyasance har yau akwai karancin gurbin da ya kamata mata su cike a mabambantan wakilci a kujeru daban daban.
Masu fashin bakin lamurran siyasa na da ra’ayin idan da mata na samun cikakken goyon bayan tsayar da su takara kuma babu tasirin addini da al’ada da dimbin nasarar da za su samu a zabe ba karama ba ce musamman bisa ga sadaukarwa da jajircewar da suke da ita.
A gwamnatance da kuma a siyasance, a kowane irin aiki a bayyane yadda aka shaidi jajirtacewa, sadaukar da kai da aiki tukuru da mata suke da shi wajen sauke muhimmin nauyin al’umma da ke kan su wanda a lokuta dama yabo da jinjinar da suke samu wajen aiwatar da gaskiya da adalci ta nunka ta takwarorinsu maza.
Juriyar tsayuwar awa da awanni a cikin rana domin jefa kuri’a, kin goyon bayan hada kai da su wajen murdiyar zabe da sadaukar da kuri’un su ga zaben ‘yan takarar da suke ganin sune maslaha kuma mafita ga al’umma abubuwa ne da mata suka ciri tuta a kai.
Duk da haka yau a siyasance mata na dauke da takaici da haushin yadda aka mayar da su saniyar ware ba tare da godiya, yabawa da sakawa halasci da amanar da suke da ita ta tsayawa kan daka wajen tabbatar da nasarar daya jinsin a kowane irin zabe.
A wurare da dama mata na fuskantar kalubalen tasirin addini da al’ada wajen hana tsayar da su takara ta yadda suke fuskantar karancin goyon baya daga jama’a da kuma jam’iyyun siyasa.
Alkaluman bayanai sun nuna a zaben 2023 da ya gabata kaso 9 ne cikin 100 suka kasance mata wanda a kowane zabe adadin raguwa yake yi tun daga zaben 2011.
A zaben 2023, an samu ‘yan takara maza 13, 725 yayin da aka samu mata 1, 544 kacal kama daga kan takarar shugaban kasa, gwamna, ‘yan majalisar dokoki na jiha da ‘yan majalisar wakilai da na dattawa.
Haka ma mafi yawan matan da ke tsayawa takara suna tsayawa ne a karkashin inuwar kananan jam’iyyu wadanda ba su da tasirin lashe zabe a Nijeriya wadda matsala ce mai zaman kan ta rashin damar da ba su samu a manyan jam’iyyu.
Nijeriya wadda ke da jihohi 36, babu jiha daya a yau da mace ke rike da kujerar shugabanci a matsayin gwamna. Haka ma a Majalisar Dattawa ta 10 wadda ke da masu shata dokoki 109, uku ne kawai mata. Dukkanin matan da suka zauna a majalisa ta tara sun fadi zaben da ya gabata.
A majalisar wakilai kuwa wadda ke da ‘yan majalisa 360, 13 ne kawai mata wanda cikin ma an samu kari ne a kan adadin mata da suka wakilci al’umma a majalisar wakilai ta tara.
Mace mai kamar maza, Dame Birginia Ngozi Etiaba ita kadai ce mace daya tilo da ta samu nasarar zama gwamna a Nijeriya a inda ta kasance mace mafi daraja ta daya a Jihar Anambra a 2006 bayan da majalisar dokokin jihar ta tsige gwamna Peter Obi, a matsayin ta na mataimakiyar gwamna sai ta gaje shi.
A tsayin shekaru mata da dama a siyasar Nijeriya sun rika kuka da zargin cin zarafi daga takwarorinsu daga shugabannin da ke jagorantar gwamnatoci da hukumomi.
A baya bayan nan a shekarar 2020 tsohuwar shugabar rikon kwarya a hukumar raya yankin Neja- Delta (NDDC) Joy Nunieh ta zargi ministan harkokin yankin, Godswill Akpabio da cin zarafin ta lamarin da ya tayar da kura a wancan lokacin.
Haka ma a 2016 Jakadan Kasar Amurka a Nijeriya James Entwistle ya zargi wasu ‘yan majalisar wakilai uku a Nijeriya da cin zarafin wata baiwar Allah ta hanyar yunkurin yi mata fyade.
A kwanan nan kuma zargin cin zarafin da Sanata Natasha Akpoti- Uduagan da ke wakiltar Kogi ta tsakiya a majalisar dattawa ta yi wa shugabar majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya tayar da hazo da haifar da cece- kuce a farfajiyar siyasar ciki da wajen kasar nan.
Hayaggar Natasha da Akpabio ya bude sabon babin kurji da damuwar da mata da yawa suke da na zargin cin zarafi daga shugabanni, haka ma hakan ya kara zama hujjar da magabata, shugabannin addini da mazajen mata ke kafewa a kai na kin baiwa mata damar shiga a dama da su a harkokin siyasa.
Watsi da korafin da Sanata Natasha ta gabatar a majalisa domin binciken zargin badakalar da juya mata baya da mafi yawan takwarorinta ‘yan majalisar suka yi da dakatar da ita na tsayin watanni shida abubuwa ne da al’umma ke kafewa a kan gwagwarmayar harkokin siyasa ba na mata ba ne duk kuwa da amana da nasarar da suke samu ta zarta ta takwarorinsu maza.
Ba shakka idan aka yi la’akari da gagarumar muhimmiyar rawar da mata ke takawa a siyasar Nijeriya, kai tsaye za a iya cewa sun cancanci samun damar rike akalar rike kowane irin shugabanci wanda ko za a samu sauyin karin adadin mata a madafun iko a 2027 da raguwar cin carafinsu da suke zargi? Lokaci zai yi alkalanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp