Kalmar demokuradiyya kalma ce da jagoran ‘yan awaren Taiwan Lai Ching-te ke yawan ambata, amma aikin da ya yi bai bi hanyar demokuradiyya ba. A baya-bayan nan, Lai Ching-te ya gabatar da wani shirin neman ‘yancin kan Taiwan, har ma ya ce wai Taiwan wata kasar demokuradiyya ce mai mulkin kanta. Lai Ching-te ya kan yin amfani da demokuradiyya don ya cuci jama’ar yankin Taiwan da sauran kasashen duniya, amma a wannan karo kowa ya san yunkurinsa na neman mulki irin na kama karya ta hanyar demokuradiyya.
Ya kamata a yi amfani da demokuradiyya don tabbatar da hakkin jama’a, a maimakon kawo illa ga hakkin jama’a. Jama’ar yankin Taiwan suna neman zaman lafiya, da samun ci gaba, da yin mu’amala, da kuma yin hadin gwiwa. Bisa binciken shekara kan huldar dake tsakanin bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan da kafofin watsa labaru na yankin Taiwan suka bayar a shekarar 2024, kashi 87 cikin dari na jama’ar yankin Taiwan sun yi tsammanin cewa, akwai bukatar kiyaye yin mu’amala a tsakanin bangarorin biyu na mashigin tekun Taiwan. Amma tun lokacin da mahukuntan jagoran ‘yan awaren Taiwan Lai Ching-te suka kama aiki a watan Mayu na shekarar bara, sun yi amfani da hanyoyin ayyukan gwamnati da dokoki da kafofin watsa labaru don hana yin mu’amala a tsakanin bangarorin biyu na mashigin tekun Taiwan.
Mahukuntan Lai Ching-te sun yi aika-aikar da ta janyo koma baya a tarihi da keta ‘yanci da hakkin dan Adam na jama’ar yankin Taiwan, kana tana son shigar da jama’ar cikin ayyukan ‘yan awaren Taiwan, da bayyana cewa wai yankin Taiwan muhimmin yanki ne da ke tabbatar da demokuradiyya a duniya. Yunkurinsa na neman ‘yancin kan Taiwan wanda ya keta bukatun jama’a da demokuradiyya ba zai samu nasara a tarihi ba. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp