A yadda na fahimci Sinawa, mutane ne da suka fahimci zamaninsu ta hanyar amfani da wayewar zamanin magabatansu. Kamar maganar ta zamo a dunkule ko? Abin da nake nufi shi ne, Sinawa sun fahimci muhimmancin wayewar kan magabatansu, don haka suka nace da bincike a kan kayayyakin tarihinsu tare da amfani da abubuwan da suka gano wajen zamanantar da kasarsu da kuma kara tabbatar da asalin tarihinsu.
Wasu abubuwa da aka gano na tarihi bisa amfani da ilimin kimiyyar kayan tarihi a ’yan shekarun nan a sassan kasar Sin sun kara fahimtar da Sinawa asalin tsohon tarihinsu, tare da yin amfani da kayayyakin bincike na zamani wajen gano tushen wayewarsu da ta kunshi samuwar dan’adam da kuma aikin gona.
- Kwamishinan Tsaron Cikin Gida Na Kano Ya Yi Murabus Watanni 7 Bayan Naɗa Shi
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [18]
Akwai wasu kokunan kawunan mutane guda uku da aka gano a birnin Shiyan na lardin Hubei da ke tsakiyar kasar Sin, wadanda bincike ya gano tabbas dan’adam ya taba rayuwa a doron kasa a yankin kasar Sin tun fiye da shekaru miliyan da suka gabata.
Babba daga cikin kokunan kawunan wadanda aka yi wa lakabi da “Dan’adam na Yunxian” da aka gano a watan Disamban 2022, ya kasance daya daga cikin sassan jikin dan’adam mafi adanawa da aka taba ganowa a daukacin yankin Turai da na Asiya. Tawagar da ta gano kokon kan a karkashin kasa ta yi amfani da ingantacciyar na’urar 3D mai tantance gaskiyar wanzuwar abu, wajen sake fasalta fuskar mai kokon kan, inda hakan ya taimaka da wasu bayanai a fannin binciken samuwar dan’adam a doron kasa da kuma yanayin ci gaban bil’adama a farko-farkon zamani.
Kazalika, gagarumar nasarar da Sinawa suka samu a wurin binciken tarihi na Shangshan da ke lardin Zhejiang a gabashin kasar Sin ta sake tabbatar da cewa, kasar Sin ce ta fara noman shinkafa a duniya. Masana kimiyyar tarihi sun gano burbushin shinkafar da aka yi imanin ta kai tsawon shekaru 10,000 a duniya, a wurin binciken. Wannan ya nuna irin rawar da magabatan Sinawa suka taka wajen aikin gona da kuma wayewar kan dan’adam a gabashin duniya.
Har ila yau, masu bincike sun gano wasu tsoffin dabarun hana koguna da madatsun ruwa ambaliya da yadda aka tsaga manyan hanyoyin ruwa da aka yi amfani da su shekaru 5,000 da suka gabata, a wani tsohon yanki na Zhejiang ta hanyar amfani da kayan binciken muhalli. Binciken ya fayyace wayewar kai na tsara birane da kula da koguna da hanyoyin ruwa irin na Liangzhu a tsohon zamani.
Babu shakka, amfani da wayewar kan magabata a zamaninmu na yanzu yana daga cikin sirrin nasarorin da Sinawa ke samu ta fuskar wayewar kai da bunkasa ci gaban kimiyya da fasaha da kere-kere da kirkire-kirkire. Ina fatan kasashenmu na Afirka su dau hannu domin jifar tsuntsu biyu da dutse daya, tabbatar da tarihinmu na asali, da amfani da wayewar kan magabata wajen samun ci gaba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp