Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin He Yadong, ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da ya dace da kasuwa, da doka da kuma mizanin kasa da kasa.
He Yadong ya bayyana haka ne a gun taron manema labarai na yau da kullum, inda ya ce, a wannan lokaci da ake ciki, wasu manyan jami’an kamfanonin kasa da kasa na kawo ziyara kasar Sin. Kuma kamfanonin sun yi nuni da cewa, babbar kasuwa, da cikakken tsarin masana’antun samar da kayayyaki, da kuma karfin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na Sin, dukkansu babbar dama ce a gare su, kuma zuba jari a Sin yana nufin cin gajiyar wannan dama.
Bugu da kari, He Yadong ya ce, bangaren Sin ya tsaya tsayin daka kan adawa da matakin karin haraji da bangaren Amurka ya dora wa Sin, yana kuma adawa da siyasantar da batun tattalin arziki da cinikayya ko amfani da shi a matsayin wani makami.
Game da kakaba karin haraji da bangaren Amurka ya yi, kakakin ya ce bangaren Sin ya riga ya shigar da kara a karkashin tsarin warware rikici na hukumar WTO, kuma zai ci gaba da bin matakai bisa ka’idojin WTO.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp