Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta fitar Litinin din nan sun nuna cewa, yawan karuwar kayayyakin da masana’antun kasar Sin suka samar, abin da ke zama wani muhimmin ma’aunin tattalin arziki, ya karu da kashi 3.5 cikin 100 a cikin watanni 7 na farkon bana.
A cewar hukumar, a cikin watan Yuli kadai, yawan kayayyakin da masana’antun Sin suka samar, ya karu da kashi 3.8 bisa dari kan makamancin lokaci na bara, kana ya karu da kashi 0.38 bisa na watan Yuni.
Daga cikin manyan sassa guda uku, samarwa da fitar da kayayyakin masarufi, sun nuna saurin bunkasuwar kashi 9.5 cikin 100 a shekara a cikin wannan lokaci, wanda ya zarce bangaren ma’adinai da na kere-kere.
Hukumar ta kara da cewa, bangaren kere-kere na zamani, ya yi fice tare da samun bunkasuwa bisa makamancin lokaci na bara, da kashi 5.9 cikin 100, da kashi 2.1 fiye da ci gaban da ake samu a masana’antun baki daya.
Dangane da kayayyakin kuwa, yawan motoci masu amfani da sabbin makamashi da batura masu aiki da hasken rana, sun karu da kashi 112.7 da kuma kashi 33.9 bisa dari a shekara, bi da bi.
Kakakin hukumar Fu Linghui ya bayyana cewa, kasar Sin za ta fadada zuba jarin samar da ababen more rayuwa, domin kara samun bunkasuwar zuba jari a masana’antun da suka dace, tare da aiwatar da manufofi na rage haraji da kudaden da ake kashewa, don rage tsadar kayayyaki ga kamfanoni a mataki na gaba.(Ibrahim)