• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Bindiga A Ƙarƙashin Jagorancin Turji Sun Kashe Manoma 12 A Sokoto

by Sulaiman
6 months ago
Sokoto

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton a karkashin Bello Turji wanda ake nema ruwa a jallo suke, sun kashe mutane 12 a garin Lugu da ke karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Majiyoyi sun shaida wa LEADERSHIP a ranar Alhamis cewa, an kai harin ne a lokacin da ’yan bindigar ke dawowa daga ziyarar Sallah a daya daga cikin al’ummar karamar hukumar Isa, inda suka harbe manoman.

  • Nasara A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda: Tattalin Arziƙin Jihar Zamfara Na Ƙara Haɓaka – Gwamna Lawal 
  • Trump Ya Ƙaƙaba Wa Nijeriya Da Ƙasashen Duniya Haraji

Dan majalisa mai wakiltar Sabon Birni a majalisar dokokin jihar, Hon. Aminu Boza, ya ce wasu mutanen yankin ne suka sanar da shi harin, amma babu labarin cewa Turji ya ziyarci wata al’umma a mazabarsa domin yin bikin Sallah.

LABARAI MASU NASABA

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Ya ce, “Akwai rahoton cewa Turji ya shirya zai ziyarci yankin Gabashin Gatawa domin gudanar da bukukuwan Sallah, amma matakin da jama’a suka dauka na sanar da jami’an tsaro ya dakatar da shi ga hakan.

“Wannan na iya zama dalilin da ya sa Bello Turji ya huce fushinsa a kan manoman da ba su ji ba gani ba.”

Sai dai hukumomin ‘yansanda a jihar sun ki cewa komai kan lamarin.

Majiyar ‘yansandan ta yi ikirarin cewa, “tunda ana ci gaba da aikin hadin gwiwa na sojoji a yankin, ‘yansanda ba su da hurumin yin magana kan ci gaban tsaro a yankin.

Da aka tuntubi runduna ta 8 ta sojojin Nijeriya ta mika wakilinmu ga rundunar ‘Operation FASAN YAMMA’, wanda har yanzu bai amsa bukatar wakilinmu ba kan bukatar tabbatar da lamarin harin har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC
Labarai

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati
Labarai

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
Next Post
Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Gyara Kuskurenta Na “Kakaba Haraji Ramuwar Gayya”

Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Gyara Kuskurenta Na “Kakaba Haraji Ramuwar Gayya”

LABARAI MASU NASABA

Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.