Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a ranar Alhamis, ya yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta na cewa ya faɗi warwas a makon jiya a wani taro.
Wike, wanda tsohon Gwamnan Jihar Ribas ne ya bayyana haka ne yayin da yake duba wasu ayyuka guda 4 da ke gudana a babban birnin tarayya Abuja, ciki har da cibiyar taron kasa da kasa da ke Abuja.
Wike ya bayyana jita-jitar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta a matsayin aikin abokan hamayya masu kokarin bata masa siyasa domin cimma wasu ‘yan bukatunsu.