Fc Barcelona za ta karbi bakuncin Borrusia Dortmund a filin wasa na Luis Companys dake birnin Barcelona a wasan zagaye na farko na kusa da na kusa da na karshe na gasar Zakarun Turai (UEFA).
Wasan da za a buga da misalin karfe 8 na dare agogon Nijeriya zai kasance wata manuniya ga dukkan kungiyoyin biyu dangane da ko zasu iya tabuka abin azo a gani a wannan kakar wasanni ta bana.
- Tattalin Arzikin Sin Na Bunkasa Yadda Ya Kamata Duk Da Kakkaba Mata Karin Harajin Kwastam Daga Amurka
- Ibas Ya Naɗa Ciyamomi A Ƙananan Hukumomin Ribas Duk Da Umarnin Kotu
Kungiyoyin biyu sun hadu a zagayen rukuni na gasar inda Barcelona ta doke Dortmund da ci 3-2, duk wanda ya samu nasarar tsallakawa zuwa matakin na kusa da na karshe zai hadu da PSG ko Aston Villa.
Kungiyoyin biyu sun hadu sau 6 a tarihi, Barcelona ce ta samu nasara akan Dortmund sau 4 a tarihi yayin da aka buga canjaras a wasanni 2, Dortmund ba ta taba samun nasara akan abokan karawar ta su ta yau ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp