• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministan Yaɗa Labarai Ya Zayyana Wa Masu Zuba Jari Na Faransa Irin Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Nijeriya

by Sulaiman
7 months ago
Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasar Faransa, inda ya jaddada masu irin sauye-sauyen tattalin arziki masu ƙayatarwa, damar kasuwanci mai faɗi da yanayin da ya dace da masu zuba jari yanzu a Nijeriya, a wani yunƙuri na Gwamnatin Tarayya na ƙara janyo jarin ƙetare na dogon lokaci.

 

A sanarwar da Rabiu Ibrahim, Mai Taimaka wa Ministan kan Harkokin Yaɗa Labarai, ya bayar, Idris ya bayyana ƙudurin sa na zurfafa dangantakar tattalin arziki da Faransa yayin da yake magana a Taron Kasuwanci na Nijeriya da aka gudanar a birnin Paris a ranar Alhamis.

  • An Kaddamar Da Bikin Nuna Fina-Finan Sinanci Na CMG Karo Na 5
  • Huawei Ya Daddale Yarjejeniya Da Kenya Don Habaka Kwarewar Ma’aikatan Kasar A Fannin Dijital

Taron, wanda kamfanin Business France ya shirya, ya samu halartar kamfanonin Faransa fiye da 200 tun a shekarar 2023.

 

LABARAI MASU NASABA

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

Idris ya gode wa kamfanonin Faransa da suka daɗe suna aiki a Nijeriya, irin su TotalEnergies, Lafarge, Peugeot, Danone, Alstom, Schneider Electric da sauran su, saboda gudunmawar da suke bayarwa a sassa daban-daban na ƙasar nan kamar makamashi, ababen more rayuwa, noma, lafiya da masana’antu.

 

Idris ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Nijeriya tana kan “tafarkin sauyi da ba a taɓa ganin irin sa ba” wanda Ajandar Sabunta Fata ke ɗauke da shi.

 

Ya ce: “Waɗannan sauye-sauyen tarihi na gina tattalin arzikin da ya fi gasa, mai gaskiya da amfanar masu zuba jari, suna mayar da Nijeriya ƙofar shiga kasuwar masu saye ta Afirka wadda ke bunƙasa, ƙarƙashin Yankin Ciniki Cikin ’Yanci na Nahiyar Afirka (AfCFTA).”

 

Wasu daga cikin sauye-sauyen da ya yi nuni da su sun haɗa da:

 

Daidaita tsarin musayar kuɗi, cire tallafin mai domin daƙile asara, tsarin farashin wutar lantarki da ya dace domin ɗorewar sabis.

 

Sauran sun haɗa da sauye-sauyen haraji da ke inganta gaskiya da sauƙaƙe kasuwanci, sababbin dokoki da tsare-tsaren kuɗi da ke ba da goyon baya ga masu zaman kan su, sauƙaƙe harkokin shigo da kaya ta hanyar National Single Window, da sauye-sauyen dijital ciki har da tsare-tsaren shige da fice.

 

Ministan ya ce Nijeriya tana da fa’ida ta musamman ga masu zuba jari: ita ce mafi girman tattalin arziki a Afirka, yawan jama’a fiye da miliyan 220 — fiye da kashi 70 nasu kuma matasa ne ‘yan ƙasa da shekaru 35 — da kuma shekaru sama da 26 na dimokiraɗiyya ba tare da katsewa ba.

 

Ya ƙara da cewa gwamnati tana tabbatar da cewa tattalin arzikin ƙasar yana gudana ne ƙarƙashin ƙa’idojin doka, tare da tallafin hukumomin da suka haɗa da CBN, NIPC, SEC, da FCCPC.

 

Ministan ya ce a cikin watanni 20 kacal da gwamnatin Tinubu, an sauya tsarin kuɗi na ƙasa, inda aka samu ƙaruwa da kashi 3.84 na GDP a zangon farko na shekarar 2024, da samun ƙarin kuɗin shiga fiye da kashi 20, tare da rage yawan kuɗin da ake kashewa wajen biyan bashi.

 

Ya ce: “Gwamnatin ta kasance mai ƙarfafawa wajen haɓaka sashen masu zaman kan su ta hanyar wasu muhimman shirye-shirye kamar Asusun Raya Ababen More Rayuwa na Sabunta Fata (RHIDF), Hukumar Bai wa Jama’a Lamunin Kaya ta Nijeriya (CrediCorp), Shirin Fadar Shugaban Ƙasa na CNG, Asusun Zuba Jari na Gidaje na MOFI (MREIF), da wasu da dama.

 

“Waɗannan shirye-shiryen suna shimfiɗa tubalin da za a iya dogaro da shi wajen jawo zuba jari na tiriliyan-triliyan na naira daga sashen masu zaman kan su a fannonin ababen more rayuwa, lamunin kayan masarufi, kiwon lafiya, gidaje, da sauran su.”

 

Ya kuma bayyana cewa bankunan Nijeriya suna ƙara faɗaɗa zuwa Turai, ciki har da buɗe ofisoshi a birnin Paris, yana mai cewa Nijeriya za ta ƙara samun wakilci a Faransa ta fannoni kamar ƙere-ƙere, fasaha da yaɗa labarai.

 

Ya gayyaci kamfanonin Faransa — musamman masu sha’awar harkar noma — da su ci gajiyar sababbin damarmakin da ke akwai a sashen kiwon dabbobi na Nijeriya, inda sabuwar Ma’aikatar Raya Kiwon Dabbobi ta buɗe ƙofofin sababbin haɗin gwiwa.

 

Ya ce: “Dole ne mu shirya wa gaba da ƙwazo da fata mai kyau, tare da ƙarfin gwiwar da kakannin mu suka nuna.”

 

A yayin zaman sa a Paris, Minista Idris zai gana da manyan hukumomin yaɗa labarai da al’adu na Faransa, kamar France Médias Monde, ARCOM, Ma’aikatar Al’adu, da Thomson Broadcast, domin ƙarfafa dangantaka tsakanin Faransa da Nijeriya a fannin watsa shirye-shirye da yaɗa labarai.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya
Manyan Labarai

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?
Manyan Labarai

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025
Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 
Manyan Labarai

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Next Post
Gobara Ta Ƙone Shaguna 12 A Kasuwar Siminti Ta Oyo

Gobara Ta Ƙone Shaguna 12 A Kasuwar Siminti Ta Oyo

LABARAI MASU NASABA

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025
Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.