Kasar Sin ta yi amanna da zaman lafiya da samun moriyar juna da ci gaba tare ta hanyar hadin gwiwa a kokarin tabbatar da gina al’umma mai makoma ta bai-daya tare da kasashe makwabta har ma da na nesa.
Domin yaukaka zumunci da kokarin bude wani sabon babi na ayyukan ci gaba tare da makwabtanta, yayin da duniya ke ci gaba da watangaririya a cikin rashin tabbas saboda bahallatsar Amurka, a kwanan kasar Sin ta karbi bakuncin wani babban taro game da ayyukan da suka shafi kasashe makwabta. Kana Shugaba Xin Jinping yana ziyarar aiki a wasu kasashe makwabta da ke yankin kudu maso gabashin Asiya har ma a yau Laraba ya isa kasar Malaysiya inda ya gana da sarkin kasar, Sultan Ibrahim Sultan Iskandar.
- Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N835 Kan Kowace Lita
- Ina Da Ƙwarewar Da Zan Iya Zama Shugaban Ƙasar Nijeriya – Makinde
Ganawar shugaba Xi da Sultan Ibrahim ta kunshi muhimmanta batutuwa da suka shafi zurfafa amincewa da juna a fannin siyasa, da cimma muhimman muradun kasashensu da kuma goyon baya ga juna a kan abubuwan da ke ci masu tuwo a kwarya.
Kasar Sin ta kuma nuna aniyarta ta lale marhabin ga shigar da karin kayan amfanin gona masu inganci na Malaysiya zuwa katafariyar kasuwarta inda ta kuma nemi kasar ta Malaysiya ta kara bai wa kamfanoninta kwarin gwiwar zuba jari a kasar.
Kasar Malaysiya ta san irin alheran da kamfanonin Sin suke ci gaba da kawo mata wajen raya tattalin arziki da ci gaban masana’antunta. Wannan ya sa Sultan Ibrahim ya bayyana cewa, Malaysiya tana dora fifiko sosai a kan zumuncinta da kasar Sin, kuma za su ci gaba da yin aiki tare domin samun nasara ga kowane bangare, tare da kara matsa kaimi ga gina al’umma mai makoma ta bai-daya a karkashin ingantattun manyan tsare-tsare kuma a duk wani sauyi da za a iya samu a duniya.
Tabbas, Malaysiya tana shaida irin ci gaban da kamfanonin kasar Sin suke kawo mata. Babban jami’in kasuwanci na tashar teku ta Kuantan, Mazlim Husin, ya bayyana yadda yankin masana’antu na hadin gwiwar Sin da Malaysiya (MCKIP) ya bude sabon babi ga bunkasa ci gaban Kuantan tun bayan kaddamar da shi a shekarar 2013. Kafa kamfanin mulmula karafa na Alliance Steel ya kara wa sauran kamfanoni kwarin gwiwar bude rassansu a yankin masana’antun wanda ya habaka samar da ayyukan yi da walwalar al’ummar wurin.
Kasar Sin ta kasance kasar da ta fi kowace kasa zuba jari a Malaysiya, inda ko a bara ta zuba kimanin dala biliyan 6.4 a kasar wanda ya kai kaso 16 na kudin shigar da Malaysiya ke samu daga zuba jarin kasashen waje kuma ana sa ran ya samar da sabbin guraben ayyukan yi 20,000.
Kazalika, wani jami’in ofishin jakadancin Malaysiya mai kula da zuba jari dake Guangzhou, Safwan Nizar Johari ya tabbatar da cewa akwai karin kamfanonin Sin dake zuba jari a kasar musamman a bangaren motocin sabbin makamashi, wanda hakan na nuna zumunci mai kyau tsakanin Sin da makwabtanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp