• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsohon Minista Ya Zargi Isra’ila Da Kasashen Yammacin Turai Da Kitsa Kashe-kashen Rayuka A Nijeriya 

by Sulaiman
7 months ago
Minista

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi kakkausar suka dangane da yawaitar kashe-kashen da ake yi a jihar Filato da sauran sassan Arewacin Nijeriya, inda ya dora laifin kitsa tashe-tashen hankula da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya.
A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Fani-Kayode ya yi ikirarin cewa wadanda ke haddasa tashe-tashen hankula ba wai kawai ’yan tada kayar baya ba ne, a’a, wasu ‘yan kasashen waje ne da ake zargin suna shigowa Nijeriya ta kan iyakokin kasar, da nufin raba kan al’ummar kasar ta hanyar addini da kabilanci.
  • Hadin Gwiwar Kasashen Asiya Da Afirka Na Habaka Karfinsu Na Dogaro Da Kai Da Cin Moriya Tare
  • Yaukaka Zumunci Da Makwabta A Aikace Tsakanin Sin Da Malaysiya
“Suna shigowa su yanka mutanenmu, suna kashe Kirista da Musulmi, ’yan Arewa da ’yan Kudu,” inji shi. “Suna so su hargitsa kasar nan, kuma su bata sunan gwamnati, an taba kitsa irin hakan kuma har yanzu ana sake kitsa hakan.”
Da yake zayyana makamancin haka, Fani-Kayode ya yi gargadin cewa, rikicin da ake fama da shi na da kamanceceniya da yadda aka kirkiri tashe-tashen hankula a zabukan shekarar 2015, inda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fuskanci irin wannan tashin hankali.
“Haka aka shirya a shekarar 2014 kafin a kayar da Goodluck Jonathan, yanzu kuma sun fara shirin irin haka domin tunkarar 2027,” in ji shi. “Mun san su wane ne, kasashen waje daga cikin kasashen Yamma da Isra’ila da wasu da dama. Ba sa son kwanciyar hankali a Nijeriya.”
Fani-Kayode ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da na tarayya da su kara daukar kwararan matakai. Ya bukaci gwamnatin jihar Filato da ta kara kaimi sosai sannan ya bukaci da a kara sa ido kan iyakokin Nijeriya.
Ya karkare da sakon hadin kai da juriya da kishin kasa, “Nijeriya za ta ci gaba da wanzuwa, Nijeriya ba za ta fadi ba, za mu taka matsayi kan matsayi, kuma dimokuradiyyarmu za ta dore da nufin Allah, kuma mu tsaya a dunkule wuri daya. Allah ya tsare Nijeriya.”
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima
Manyan Labarai

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

November 1, 2025
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
Manyan Labarai

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

November 1, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
Manyan Labarai

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Next Post
Bai Wa Shanu Guba: Sojoji Sun Shiga Tsakani Domin Dakile Yunkurin Ramuwar Gayya A Filato

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

November 1, 2025
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

November 1, 2025
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.