Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya amsa tambayoyin da aka yi masa a jiya Jumma’a game da binciken da Amurka take yi kan kasar Sin bisa ayar dokar kasuwanci mai lamba 301 kan bangaren ayyukan teku, da jigilar kayayyaki, da gina jiragen ruwa.
Kakakin ya ce, Amurka ta dauki matakin sanya shingaye a wadannan bangarori na kashi-kai, kuma kasar Sin na matukar nuna rashin jin dadi da kuma kin yarda da lamarin.
Jami’in kuma ya kara da cewa, matakin da Amurka ke dauka ba shakka manufa ce ta kare kai da kariyar cinikayya marasa kima, kuma ba komai ba ce illa nuna wariya da kuma illata tsarin ciniki tsakanin mabambantan bangarori bisa tushen ka’idoji da kyakkyawar zamantakewa da dokar cinikayya ta duniya. Sin kuma na kalubalantar Amurka da ta mutunta bin gaskiya da ka’idar ciniki tsakanin mabanbamtan bangarori, ta daina dora laifi kan sauran kasashe, da gyara kuskurenta ba tare da bata lokaci ba.
Kazalika, ya ce, Sin za ta ci gaba da mai da hankali kan matakan da Amurka za ta dauka, kana za ta dauka matakin mai da martani don kare muradunta idan hakan ya wajaba. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp