An samu rahoton cewa, Fursunoni tara a gidan yari na Oko Erin a jihar Kwara a ranar 19 ga watan Afrilu, sun tsere.
Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa, da misalin karfe 10:00 na dare, wani ma’aikaci a gidan, mai suna Joseph Issa, ya sanar da faruwar lamarin.
- Rugujewar Gini A Legas: Adadin wadanda Suka Mutu Ya Kai Biyar, An Ceto 20
- Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Vietnam Da Malaysia Da Cambodia
Ba tare da bata lokaci ba, ‘yansanda suka yi gaggawar isa wurin, inda suka sake kama daya daga cikin wadanda suka tsere, mai suna Abdul Raman Misa mai shekaru 15. An mayar da Misa gidan yarin, yayin da ake ci gaba da neman sauran takwas din da suka arce.
A halin yanzu dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan yadda suka tsere.