Kakakin ma’aikatar kasuwancin Sin ya amsa tambayoyin da aka yi masa kwanan baya game da matakin da Amurka ta dauka na fakewa da batun harajin kwastan don tilastawa sauran kasashe kayyade cinikinsu da kasar Sin.
Kakakin ya ce, kwanan baya Amurka ta kakabawa sauran kasashe harajin kwastam yadda take so bisa hujjar “yin-min-na-rama”, a wani bangare kuwa ta tilastawa bangarori daban-daban da su kaddamar da shawarwari kan harajin kwastam na ramuwar gayya tsakaninsu da Amurka. Ba shakka matakin na matsayin babakeren da take yi ne a bangaren cinikayya da tattalin arziki bisa wannan hujja.
- Tsakanin Kafa Shingaye Da Gina Gada: Yadda Matakan Amurka Da Sin Suka Bambanta Sosai
- Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 3, Ta Wanke Gonakin Shinkafa Sama Da Hekta 10,000 A Neja
Sin ba za ta yarda a keta muradunta ta hanyar daukar matakai bisa radin kai ba. Za ta mayar da martani mai tsanani muddin Amurka ta yi hakan, ko shakka babu Sin na da niyya da kuma karfin kiyaye muradunta.
Ya kara da cewa, kowace kasa za ta yi asara idan an gudanar da cinikin duniya bisa ka’idar fin karfi. Sin na fatan kara hadin gwiwa da sauran kasashe don tinkarar kalubale tare da yaki da babakere, ta yadda za su kare muradunsu bisa adalci da daidaito.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp