Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurni a kwanan baya kan aikin inganta hadin gwiwar jama’a da sojan kasar, inda ya ce, nagartacciyar hulda mai karfi tsakanin jama’a da soja fifiko ne da bangaren siyasar Sin ya jima da shi. Ya ce ya kamata a tsaya tsayin daka kan jagorancin ra’ayin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin a sabon zamani, kuma a nace ga jagorantar jam’iyyar JKS a dukkanin fannoni, da zurfafa yin kwaskwarima, da kirkire-kirkire, da ma kyautata tsare-tsare da manufofi, har da raya aikin inganta hadin gwiwar jama’a da soja.
An kira taron rada sunan birane ko gundumomi dake taka rawar gani a wannan bangare a yau Laraba a nan birnin Beijing. Inda aka saurari muhimmin umurni da Xi Jinping ya bayar. Firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci taron tare da gabatar da jawabi. (Amina Xu)