Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda ya sanar da wasu canje-canje masu muhimmanci game da yadda ake gudanar da ayyukan aikin hajja a jihar.
Ya bayyana cewa yanzu ba za a amince da jami’an da ba su kware ba wurin rakiyar mahajjata a kasa mai tsarki.
- Zanga-zangar Lumana Wani Bangare Ne Na Mulkin Dimokuradiyya
- NLC Ta Yi Zanga-Zanga A Ofishin Wike, Ta Nemi A Biya Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi Albashin N70,000
Sanarwa ta zo ne bayan gwamnan ya amshi rahoton aikin hajjin wannan shekara daga Amirul hajj na jihar, Alhaji Tukur Ahmed Jikamshi.
Gwamnan ya bayyana cewa ba za a yi amfani da kudin al’umma ba ga mutanen da ba za su iya kula da mahajjata yadda ya kamata ba.
Gwamna Radda ya kara da cewa ya yi taro da shugabannin kananan hukumomi guda 34 domin tabbatar da cewa malaman da suka cancanta ne kadai aka zaba a matsayin masu koyarwa a ayyukan aikin hajjin bana.
Ya kuma yi alkawarin kafa kwamitin yada labarai domin yada ayyukan aikin hajjin tare da ba da kulawa ta musaman kan shawarwarin da aka bayar kan rahoton da kwamitin aiki hajjin ya gabatar.
Da yake gabatar da rahoton, tsohon mataimakin gwamnan Jihar Katsina kuma Amirul Hajj, Alhaji Tukur, ya bayyana wasu muhimman batutuwa da ke bukatar kulawa.
Ya kuma bayyana bukatar tallafa wa hukumar kula jin dadin alhazai wurin tantance malamai. Yana mai cewa mafi yawancin shugabannin kananan hukumomi sun sanya malaman da ba su da kwarewar yadda za su koyar da mahajjatan.
Amirul Hajja ya nuna damuwarsa bisa yadda ake samu wadanda ba ‘yan Nijeriya ba a cikin mahajjatan jihar tare da ba da shawarar inganta hanyoyin da ake bi wurin tantance mahajjatan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp