Biyo bayan nasarar da kungiyar Manchester United ta samu a kan kungiyar Lyon ta Faransa, inda ta samu tsallakawa matakin wasan gab da na karshe a gasar Europa, yanzu tambayar da ake yi ita ce shin za ta iya lashe gasar?
Kungiyar dai yanzu ta mayar da hankali kai tsaye wajen ganin ta lashe gasar ta Europa domin ita ce hanya daya tilo da za ta ba ta damar zuwa kofin Zakarun Turai. Tsohon dan wasan kungiyar, Darren Fletcher ya ce, dole mutum ya fara tunanin ko an rubuta sunan kungiyar a kofin na Europa (lashe kofin) bayan nasarar da ta samu a kan Lyon domin kokarin da ‘‘yanwasan kungiyar suka yi a wasan ne ya sa ya fara canja tunani.
- Rage Farashin Man Fetur Na Dangote Ya Sa Wasu Gidajen Mai Na Kullewa
- Zulum Ya Taya MNJTF Da Gwamnatin Alihini Bayan Harin Boko Haram A Wulgo
Amma zai yi wahala mutum ya tababar cewa Manchester United za ta iya lashe gasar musamman ganin yadda suka doke Lyon.
Manchester United ta kai zagayen kusa da karshe ne bayan doke Olympic Lyon ta Faransa da 5-4, bayan an yi canjaras da 2-2 a wasan farko da aka buga a Faransa. Kenan United ta yi nasara da 7-6 jimilla. Yanzu United za ta fafata wasan gab da na karshe ne da kungiyar Athletic Bilbao a ranar 21 ga watan Mayu.
Kungiyar ta Bilbao ta kai wasan karshe a gasar Europa sau biyu, na karshen a shekarar 2012, lokacin da Atletico Madrid ta doke ta da ci uku da nema a Bucharest.
Shekara 13 ke nan rabon United ta hadu da Athletic Bilbao, inda kungiyar ta Sifanya ta doke United da 2-1 a gasar ta Europa a shekarar 2012. Ita kuma United wannan ne karo na biyu da za ta buga wasan gab da na karshe a gasar Europa a shekara hudu.
A wancan karon, Manchester United ta doke Roma da ci 8:5 jimilla sai dai kungiyar Billareal ta doke ta a wasan karshe a bugun fanareti bayan an tashi wasan kunnen-doki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp