Mataimakin sakatare janar na MDD kan harkokin agaji da jin kai Tom Fletcher, ya ce kasashen duniya za su iya samun ci gaban tattalin arziki mai girma idan suka hada gwiwa bisa aminci da tuntubar juna, kamar yadda kasar Sin ke nunawa.
Tom Fletcher wanda ya ziyarci Sin a makon da ya wuce, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Juma’a cewa, irin wannan hadin gwiwa na da muhimmanci musammam a halin da ake ciki yanzu, inda tsarin agajin jin kai a duniya ke fuskantar kalubale yayin da ake tsaka da fama da rikice-rikice a yankin Gaza da kasashen Ukraine da Sudan.
- Wang Yi Ya Ce Kasar Sin Za Ta Magance Cin Zarafin Da Amurka Ke Yi Ita Kadai
- Kungiya Ta Bai Wa Marayu Tallafin Atamfofi Da Shaddodi A Yobe
Ya ce, hadin gwiwa na bukatar kowa ya kasa kunne kuma ya tofa albarkacin bakinsa, yana mai cewa dabarar kasar Sin ta hulda da kasashen duniya na nuni da hakan.
A cewarsa, kasar Sin ba ta neman kakaba akidunta kan sauran kasashe. Abun da take nema shi ne, aminci da tuntubar juna. Kuma a ganinsa, wannan shi ne ya kamata ya kasance ruhin hadin gwiwa.
Bugu da kari, ya ce shawarwarin da Sin ta gabatar game da tabbatar da tsaro da zaman lafiyar duniya da ci gaban duniya da hadin gwiwa ta fuskar al’adu, sun dace da muradun MDD na wanzar da zaman lafiya da gudanar da ayyukan agaji da tabbatar da tsaro a duniya, yana mai cewa, akwai babbar dama ta kara hadin gwiwa a cikinsu. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp