Ba shakka Amurka ta sha gaban kasashen duniya wajen mallakar masana’antun kere-kere da kiyasi mai yawa, amma fa kafin tauraronta ya fara disashewa. Yawancin Amurkawa sun yi imanin cewa Amurka na iya komawa kan kadaminta na tsohuwar daukaka, kuma hakan na da muhimmanci ga farfadowar kasar. Inda wasu daga ciki ke kafa misali da yadda Japan da Jamus suka farfado da masana’antunsu bayan yakin duniya na biyu a matsayin hujjar cewa za su iya sake gina kasar ta Amurka tare da madaidaitan manufofi da jajircewa.
A bayyane yake cewa Amurka za ta iya sake farfado da wani bangare ko wasu daga cikin masana’antunta kuma ya kamata ta yi hakan, sama da komai ma, don tallafawa kasar a matsayinta na mai samar da muhimman fasahohi da kuma tabbatar da tushen tsarin cin gashin kanta mai muhimmanci ga tsaron kasa da shirye-shiryen gaggawa, kuma tana iya yin hakan ba tare da bata lokaci mai yawa ba, ko kokarin dakile fasahohin sauran kasashe ko yake-yake na cinikayya ba. Abin da ba a bayyana ba shi ne masana’antu nawa ne Amurka za ta iya farfado da su? Bari mu fara da mahangar wadanda ke kafa misali da abin da ya faru game da farfado da masana’antun Japan da Jamus bayan yakin duniya na biyu a matsayin cewa Amurka za ta iya yin hakan. A wancan lokacin, Jamus da Japan sun riga sun kafa ingantaccen tsarin aiki na masana’antu. Kuma ga wadanda suka tsira daga yakin, da yawa sun gamsu da su yi aiki a masana’antu, inda suke samun kwanciyar hankali bayan tashin hankalin da suka fuskanta. Har ila yau, al’amarin ya kasance cewa yawancin kasashen duniya sun ci gaba da aiki don tabbatar da juyin juya halin masana’antu na biyu tare da daukar matakai da suka kai ga juyin juya halin masana’antu na uku.
- Makafi 37 Sun Zana Jarabawar JAMB A Bauchi
- Bai Dace A Mika Wuya Ga Wanda Ya Nuna Fin Karfi Da Matakan Haraji Ba
Amma a yau, ba a samu daya daga cikin wadannan yanayi na tarihi a Amurka. Bugu da kari, yana yiwuwa yawancin karfin da Amurka ke da su na iya zama tarko yanzu.
Bari mu dauki dala a matsayin misali, tattalin arzikin Amurka na dogara ne kacokan da girman dalar Amurka. Yayin da kasafin kudinta ke gazawa wajen biyan bukatunta na cikin gida, kuma tana da al’adar dogaro da kasashen waje kan kudaden da take kashewa da ke da alaka da jingina gazawar mulkinta ga sauran kasashen duniya, kamar yadda ta yi a lokacin rikicin hada-hadar kudi na duniya a shekarar 2008, ta yaya masana’antunta za su farfado bisa wannan tsarin?
Hakazalika, babu yadda za a yi Amurka ta sake zama cibiyar masana’antun duniya bayan da ta yi watsi da matsalolin da ake fuskanta a zahiri kamar sauyin yanayi, wanda ayyukan masana’antu ne suka haifar da shi tun farko. Bari mu dauka cewa Trump zai iya cimma nasarar aiwatar da manyan gyare-gyare game da tsarin kasar lokaci guda, zuwa kyakkyawan tsarin siyasa da tattalin arzikin kasar duk da cewa akwai rashin jituwa tsakanin jam’iyyun kasar. Kana bari mu dauka cewa mutanen Amurka da ma duniya baki daya za su koma sayen yawancin kayayyakin da ake samarwa a Amurka. Har yanzu an bar mu da wata tambaya, shin za a samu isassun Amurkawa da za su yarda su yi aiki a masana’antunta, kuma za su yi hakan kan albashi mara tsoka idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya, bayan da Trump ya kori kaso da dama na baki daga kasar ta Amurka? (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp