Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.
A yau shafin na mu zai kawo muku yadda za ku magance kurajen dake damun fuskarku. Matsalar kuraje da tabon fuska sun fi shafar matasa, mata da maza.
- Mataimakin Shugaban Ƙasa Zai Wakilci Nijeriya A Rantsar Da Shugaban Gabon
- Sabon Tsarin Ci Gaba Na Sin Ya Kawo Sauyi Daga Samar Da Takalma Miliyan 100 Zuwa Kera Mattarar Bayanai Ta Microchip
Wani lokaci sai an sha wahalar magance kurajen fuska, amma sai tabo ya ki bacewa.
Rashin bacewar tabo a fuska na bata kwalliya.
Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabon.
Da yawan mutane sun gwada mayukan kantin, domin rabuwa da tabon fuska.
Wasu sun yi sa’a wasu kuma ba su yi sa’a ba.
A yau mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a san cewa daya za a zaba daga cikin hanyoyin da za mu lissafo, kada a hada su gaba daya.
Domin yin hakan zai kara la’anta fuska ne.
A samu ganyen dogonyaro, sai a hada shi da kurkum, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15, sannan a wanke da ruwan dumi.
Za a iya shafa markadaddan dankalin Turawa a kan tabo.
Hakan na magance kurajen fuska, sannan ya hana su sake fitowa.
A daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabo. Tafarnuwa tana wari, amma tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.
A hada karas da tafarnuwa da zuma sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin a wanke.
A samu hodar ‘baking soda’, sai a hada ta da ruwa, sannan a shafa a fuska zuwa minti 2 ko 3, daga nan a wanke fuska da ruwan dumi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp