Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Moscow na kasar Rasha a jiya Laraba, domin fara ziyarar aiki tare da halartar bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kishin kasa na tsohuwar tarayyar Soviet.
Cikin wani rubutaccen sako da ya gabatar a filin jirgin sama na birnin, shugaban Xi ya ce kasarsa da Rasha makwafta ne na gari da ba za su rabu ba, kuma kawaye ne dake kasancewa tare duk runtsi, kana abokan hulda ne da suke cimma nasarori tare.
Ya ce yanayin ’yancin kai, da gogewa da juriyar alakar Sin da Rasha ba alfanu kadai suka haifar ga al’ummun kasashen biyu ba, har ma da samar da muhimmiyar gudummawar wanzar da daidaito bisa matsayin koli, da ingiza tsarin cudanyar duniya mai tasiri daga mabambantan sassa bisa tsari da daidaito.
Yayin ziyarar tasa, shugaba Xi zai gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, inda za su zurfafa tattaunawa game da alakar kasashen biyu, da hadin gwiwa na zahiri, da manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyyoyi da suke jan hankulan kasashensu, kana da sanya kakkarfan kuzari don bunkasa tsare-tsaren alakar kasashen biyu, bisa matsayin koli daga dukkanin fannoni a sabon zamani. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp