A baya bayan nan Amurka ta kaddamar da yakin cinikayya kan kasashen duniya, kuma tattaunawarta game da batutuwan cinikayya da sassan kasa da kasa na tafiyar hawainiya. Halayyar rashin tabbas ta Amurka ta sa al’ummun duniya nuna shakku da damuwa game da ita.
Wasu alkaluma masu kunshe da sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta tattara, sun nuna cikin masu bayyana ra’ayoyi 31,004 na sassan duniya, kaso 51.8 bisa dari na ganin sun fi cin gajiya daga cinikayya da Sin idan an kwatanta da Amurka, yayin da kaso 48.1 bisa dari, na masu bayyana ra’ayoyi daga Turai ke kallon sabuwar gwamnatin Amurka a matsayin wadda ba za a iya amincewa da ita ba.
Kuri’ar jin ra’ayin wadda kafar watsa labarai ta CGTN ta kasar Sin, da jami’ar Renmin ta kasar suka gudanar, karkashin cibiyar nazarin harkokin watsa labarai na kasa da kasa a sabon zamani, ta kunshi matsayar masu bayyana ra’ayoyi 31,004 daga kasashen duniya 41, ciki har da al’ummun kasashe masu ci gaba da suka hada da Birtaniya, da Faransa, da Australia, da na kasashe masu tasowa kamar Thailand, da Brazil, da Afirka ta Kudu, da Mexico da kasar Masar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp