Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da jagoran da ya kafa majalisar bunkasa cinikayya ta Denmark dake kasar Sin ya aike masa, yana mai karfafa gwiwar cibiyar da kamfanoni mambobinta, da su samar da sabbin gudummawar raya alakar Sin da Denmark, da kawancen Sin da Turai, kana su zurfafa hadin gwiwa na cimma moriyar juna tsakanin sassan.
Shugaba Xi ya kuma bayyana fatan cibiyar da kamfanoni mambobinta za su ci gaba da taka rawar gani, wajen karfafa cudanya tsakanin Sin da Denmark da ma tsakanin Sin da Turai baki daya, kana su ba da gudummawa wajen bunkasa fahimtar juna da abota, da zurfafa hadin gwiwar cimma moriyar juna tsakanin sassan.
A baya bayan nan, a matsayinsa, da kuma matsayin kujerarsa ta jagoranci, wanda ya kafa majalisar ya aikewa shugaba Xi wasikar taya murnar cika shekaru 75 da kafa huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Denmark, tare da bayyana fatan ci gaba da zurfafa hadin gwiwar kasashen biyu. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp