Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya gode wa kasar Sin, dangane da gudummawar da ta bayar a fannin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasarsa. Ya ce, kasar Senegal ta dauki kasar Sin a matsayin abokiya mafi muhimmanci bisa manyan tsare-tsare, kuma tana fatan kara hadin gwiwa da ita domin ci gaba da inganta huldar dake tsakaninsu, ta yadda bangarorin biyu za su cimma sabbin nasarori.
Shugaba Faye ya bayyana haka ne jiya, yayin da ya karbi takardar wakilcin kasa daga sabon jakadan kasar Sin a kasar Senegal Li Zhigang, a birnin Dakar, fadar mulkin kasar.
A nasa bangare, jakada Li ya ce, a watan Satumban shekarar da ta wuce, shugabannin kasashen Sin da Senegal sun jagoranci taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka a Beijing, inda suka cimma matsaya daya kan yadda za a raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Senegal, da kuma Sin da kasashen Afirka. Ya ce, bangarorin biyu za su bi wannan ra’ayi daya da suka cimma wajen habaka dangantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin kasashensu zuwa sabon matsayi. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp