Wata mukala ta baya-bayan nan da Mujallar kasar Amurka ta Variety Magazine ta wallafa ta bayyana yadda ake samun karuwar kasashen duniya masu rungumar masana’antar fina-finai ta kasar Sin da kuma ci gaban da masana’antar ke samu, kamar yadda aka nuna a bikin fina-finai na Cannes na shekarar 2025.
Bana an cika shekaru hudu a jere da fara kafa rumfar fina-finan kasar Sin a bikin fina-finan na Cannes.
- SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (I)
- Zargin Kin Amincewar Kwankwaso Zuwa APC: Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Mai Taimaka Ma Ta
Kamfanin shirya fina-finai na kasar Sin (CFCC) ne yake shirya rumfar a karkashin jagorancin hukumar kula da fina-finai ta kasar Sin, inda aka tattaro kamfanoni da cibiyoyin fina-finai na kasar Sin fiye da 60 domin baje kolinsu.
A cewar mujallar, rumfar ta zama wani dandali na nuna kuzari da kirkire-kirkire na masana’antar fina-finan kasar Sin, tare da karfafa hadin gwiwa tsakanin kamfanonin fina-finai na kasar Sin da na kasashen duniya. An gabatar da fiye da fina-finai 180 na kasar Sin ga masu kallo a duniya, wadanda suka kunshi nau’o’in fasahohin fina-finai da adabi, kama daga fim na kagaggun hotuna zuwa na tarihi.
Fina-finai irin su “Ne Zha 2,” da “Detective Chinatown 1900” da kuma “Creation of the Gods II: Demon Force” sun samu karbuwa daga masu sayen fina-finai na duniya.
Kamar yadda mujallar ta bayar da rahoto a kai, rumfar fina-finai ta kasar Sin ta zama wata alama da ke nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kyautata cudanyar al’adu da hadin gwiwar kasa da kasa a harkar fina-finai. Kana, bisa samun karuwar jawo hankulan kasashen duniya da kuma kafa kwakkwarar turbar fasahar kirkira ta gwaninta da iya tsara labarin fim, sashen fina-finan na kasar Sin ya mike haikan wajen taka rawa sosai a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp