Wasu masana a tarayyar Najeriya sun jinjinawa yadda Najeriya da Sin suka daga dangantakarsu zuwa huldar abota bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni a bara, matakin da ya tabbatar da goyon bayansu ga kokarin tinkarar kalubalen karin harajin kwastam da Amurka ke dora musu bisa radin kai.
Kwanan baya, an gudanar da taron tattaunawa kan yadda za a tinkari harajin kwastam da Amurka ke kakabawa sauran kasashe a birnin Abuja hedkwatar Najeriya, inda babban darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta Najeriya Charles Onunaiju ya bayyana cewa, hadin gwiwar Sin da Najeriya bisa dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka, da shawarar “ziri daya da hanya daya” da dai sauransu, ba ingiza bunkasuwar manyan ababen more rayuwa a Afirka kadai ya yi ba, har ma ya inganta karfin Najeriya da sauran kasashen Afrika, na tinkarar kalubaloli, da barazanar da Amurka ke haifarwa duniya.
Baya ga hakan, darektan cibiyar nazarin huldar Sin da Afrika a sabon zamani a jami’ar Abuja Sheriff Ghali Ibrahim, ya ce, kasuwar Afirka na da cikakken boyayyen karfi, kuma duba da yawan al’ummar Najeriya, tana da muhimmanci matuka ga tattalin arzikin Afirka, don haka sabuwar huldar da Najeriya da Sin ke kullawa, za ta yi babban tasiri ga kyautatuwar tsarin ciniki na duniya.
Dadin dadawa, babban manajan kungiyar hadin gwiwar manoman Najeriya wato NFGCS Retson Tedheke ya ce, dabaru da basirar bunkasar kasar Sin abubuwan koyi ne masu daraja ga nahiyar Afirka, kuma za su taka rawa wajen tinkarar kalubaloli bisa hadin kai. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp