Kasashen Sin da na ASEAN sun kammala tattaunawa game da kafa yankin ciniki cikin ‘yanci na Sin da ASEAN (CAFTA) karo na 3, wanda ke aikewa da sako mai karfi na goyon bayan gudanar ciniki cikin ‘yanci da hadin gwiwa mai bude kofa.
A cewar Mao Ning, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, hakika wannan labari ne mai dadi, tana cewa, wani muhimmin mataki ne na rattaba hannu kan yarjejeniyar daukaka yankin a karo na 3.
Ta kara da cewa, Sin da kasashen ASEAN, dukkansu masu goyon bayan dunkulewar tattalin arzikin duniya ne da cudanyar bangarori da dama, haka kuma yankin na CAFTA na 3, zai taimakawa Sin da kasashen wajen kara zurfafa budewa juna kofa da samun ci gaba da wadata. (Fa’iza Mustapha)














