A wani gagarumin mataki na ji kai tsaye daga bakin al’umma, Gwamnan jihar Yobe zai gudanar da tattaunawar kai tsaye da jama’a, a ranar Dimokuradiyya ta 29 ga Mayu, domin bai wa jama’a damar tuntubar ayyukan da gwamantin Mai Mala Buni ta aiwatar tare da manufofi da alkawuran da gwamnatinsa ta dauka a baya, inda a karon farko jama’a za su yi ido-da-ido da jami’an gwamnati a jihar.
Dokta Ibrahim Muhammed Yabani, Mashawarci na musamman ga Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni kan harkokin Rediyo, Talabijin, da Kafofin Sadarwa na zamani, inda ya sanar da hakan a wani taron manema labaru, a ranar Asabar a Damaturu, a shirye-shiryen bukukuwan ranar 29 ga Mayu.
- An Gano Kofin Gasar Zakarun Turai Na Mata Bayan Sace Shi Da Aka Yi
- Warware Basussuka: WAEC DA NECO Sun Saki Sakamakon Ɗaliban Zamfara Na Shekara Biyar
Ya bayyana cewa, taron zai zama kai tsaye, domin baiwa al’ummar jihar Yobe cikakkiyar damar tattaunawar kai tsaye da Gwamnan jihar, dangane da yadda al’ammuran gwamnati, ayyukan ci gaba da manufofin gwamnati mai ci yanzu.
Ya ce, taron zai kunshi ilihirin zababbun masu rike da madafun iko, da masu ruwa da tsaki a jihar, domin baiwa jama’a damar tattaunawar kai tsaye tare da gabatar da koke-koken su ko shawarwari zuwa ga gwamnati.
“Manufar wannan taron ita ce kawar da shamaki don tattaunawa tsakanin gwamnati da jama’a.”
“Kuma taron zai baiwa jama’a damar yi wa gwamna tambayoyi kai tsaye, kuma su sami bayani kan ayyukan gwamnati.”
“Wannan shi ne ci gaba a siyasance, kuma ba sabon abu bane a duniya, amma a jihar Yobe, wannan wani sabon salo ne. Mataki ne na sauke nauyi, gaskiyar da jama’a suka baiwa gwamnati, samun hadin kai, da sauran jama’a kai tsaye.” In ji shi.
Dakta Yabani ya jaddada cewa, taron an shirya shi ne domin baiwa al’ummar jihar Yobe kwarin gwiwa, a tafarkin gudanar da ayyukan da gwamnati take aiwatarwa na ci gaba da kyauta jindadin su, tare da basu dama wajen tofa albarkacin su wajen tsara manufofi gwamnati.
“Maigirma Gwamna Buni a shirye yake ya amsa duk wata tambayar da al’ummar jihar za su yi, yan jarida, da sauran kungiyoyin al’umma.” In ji Yabani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp