Shugaban kasar Kenya William Samoei Ruto ya ziyarci kasar Sin daga ran 22 zuwa 26 ga watan Afrilun da ya gabata, bisa gayyatar da takwaransa na Sin Xi Jinping ya yi masa. Yayin ziyararsa, shugabannin biyu sun kai ga matsaya daya kan daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa hulda mai makoma ta bai daya a sabon zamani. William Samoei Ruto ya shedawa manema labaran CMG cewa, dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka na FOCAC ba samar da wani dandalin mu’ammalar ra’ayoyi kadai ya yi ba, ya kuma shimfida sharadi mai kyau ga bangarorin biyu wajen fidda sabbin damammakin hadin gwiwa da samun moriya tare.
Ruto ya ce, FOCAC ya samar da wani ingantaccen dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka dake shigar da karin jari daga ketare zuwa nahiyar Afirka, matakin da ya gaggauta bunkasuwar manyan ababen more rayuwa a nahiyar, musamman a bangaren tasoshin jiragen ruwa da layin dogo da hanyoyin mota da sauransu karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, inda ya ce nasarorin da aka samu na jawo hankulan kasa da kasa.
Game da matakin kakabawa dukkan kasashe ciki hadda Kenya da takwarorinta na Afrika karin haraji da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka, masanan tattalin arziki sun bayyana shi a matsayin wanda ya sabawa dokar raya nahiyar Afirka da ba ta damammaki wato AGOA. A ganin Shugaba Ruto, dunkulewar tattalin arzikin duniya abu ne da ya zama dole ga daukacin al’ummun duniya, kuma manfunar gudanar da harkoki tsakanin mabambantan bangarori ita ce hanya daya tilo da za a bi na tabbatar da gudanar ciniki a duniya, duba da cewar tabbacin cinikin duniya ingantaccen karfi ne dake gaggauta ci gaba da bunkasuwar duniya baki daya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp