Rundunar ‘yansanda ta fara gudanar da bincike kan fashewar wani abu a mashigar babban birnin tarayya Abuja a kan hanyar Mararaba zuwa Nyanya a ranar Litinin.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu rahoton kiran gaggawa a ranar 26 ga watan Mayun 2025 da misalin karfe 2:50 na rana, dangane da fashewar wani abu a kan hanyar.
- Sin Za Ta Harba Na’urar Binciken Samaniya Ta Tianwen-2
- FCTA Ta Rufe Hedikwatar PDP Ta Ƙasa Saboda Ƙin Biyan Harajin Ƙasa
“Bayan samun rahoton, nan take aka tura jami’an sashin warware bama-bamai (EOD) inda lamarin ya afku, cikin gaggawa aka killace yankin da lamarin ya shafa domin tantancewa da bincike don tabbatar da tsaron lafiyar matafiya da mazauna wurin,” in ji SP Adeh.
Adeh ya kara da cewa, an ceto wani da lamarin ya rutsa da shi kuma ba tare da bata lokaci ba, aka kai shi Asibiti wanda a halin yanzu, yana samun kulawar likitoci.
Rundunar ‘yansandan ta kuma kara da cewa, “An fara gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abinda ya fashe da kuma musabbabin fashewar.
Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, ta bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu, su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da fargaba ba, tare da tabbatar da cewa babu wata fargaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp